Yanzu-yanzu: Majalisar zartaswa ta fitar da $3.1bn don bunkasa hukumar Kwastam

Yanzu-yanzu: Majalisar zartaswa ta fitar da $3.1bn don bunkasa hukumar Kwastam

- Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da fitar da $3.1bn don daga darajar hukumar kwastam ta Najeriya

- Ministar kudi, Zainab Ahmed, ce ta bayyana hakan a karshen zaman majalisar zartarwa na yanar gizo da aka yi a Abuja a yau Laraba

- Ta ce yarjejeniyar ta tsawon wa’adin shekaru 20 ne kuma kudin zai fito ne daga masu zuba jari da kudaden shiga da ake sa ran samu daga wannan bangare wanda ya kai dala biliyan $176

Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da fitar da dalar Amurka biliyan $3.1 don daga darajar hukumar kwastam ta Najeriya (NCS).

Ministar kudi ta kasa, Zainab Ahmed, ce ta bayyana hakan a karshen zaman majalisar zartarwa na yanar gizo da aka yi a Abuja a yau Laraba, 2 ga watan Satumba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

A cewarta, yarjejeniyar ta tsawon wa’adin shekaru 20 ne kuma kudin zai fito ne daga masu zuba jari da kudaden shiga da ake sa ran samu daga wannan bangare wanda ya kai dala biliyan $176.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel