Na’Abba: Idan har Ibo su ka zakulo wanda ya cancanta, to zan mara masu baya

Na’Abba: Idan har Ibo su ka zakulo wanda ya cancanta, to zan mara masu baya

A ranar Talata ne tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Umar Ghali Na’Abba, ya yi magana game da babban zabe mai zuwa na 2023.

Ghali Umar Na’Abba ya bayyana cewa zai goyi bayan mutumin Ibo, muddin aka dauko wanda ya cancanta a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Jaridar Vanguard ta rahoto Hon. Ghali Umar Na’Abba ya na bayyana wannan a lokacin da shugaban kungiyar NPEM, Chibuzor Okereke, ya kai masa ziyara.

Na’Abba ya ce: “Wasu daga cikin manyan abokan da na ke da su, sun fito ne daga yankin Kudu maso gabas, wadanda a shirye su ke su mara mani baya ko yaushe.”

Tsohon ‘dan majalisar ya tabo tarihi, inda ya tunawa ‘Yan Najeriya cewa saura kiris Marigayi Alex Ekwueme ya zama ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 1999.

A cewar ‘dan siyasar, abin da ya hana ‘dan takararsu watau Alex Ekwueme samun tikiti shi ne goyon bayan da sojoji su ka ba abokin adawarsa (Obasanjo).

KU KARANTA: APC ta yi tanadi, ta rubuta sakamakon zaben Edo na karya – PDP

Na’Abba: Idan har Ibo su ka zakulo wanda ya cancanta, to zan mara masa baya
Na’Abba ya na ganin irinsu Ken Nnamani sun dace da mulki
Asali: UGC

Ya ce: “A yau akwai tulin ‘yan siyasa da su ka cancanta a kirar Sanata Ken Nnamani, Pius Anyim da su ka fito daga Kudu maso gabas da za su iya rike kasarmu.”

“Idan su ka kawo wadanda ba su cancanta, za su bata garinsu a 2023, idan su ka kawo wadanda su ka dace, zan goyi bayan Kudu maso gabas.” Inji Hon Na’Abba.

A jawabinsa, Chibuzor Okereke ya yabawa Ghali Umar Na’Abba wanda ya kira mutum mai adalci.

Shi ma wani tsohon mai ba Ibrahim Shekarau shawara, Shuaib Mustapha Kano ya fito ya bayyana irin haka, ya ce lokaci ya yi da za a jarraba Ibo da rike kasar nan a 2023.

Alhaji Shuaib Mustapha Kano ya taba zama mai ba tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai-ci, shawara a kan harkar siyasa, ya na ganin zai yi kyau Ibo su taba mulki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng