Kotu ta garkame kakakin jam'iyyar PDP a kan kalubalantar gwamnatin APC

Kotu ta garkame kakakin jam'iyyar PDP a kan kalubalantar gwamnatin APC

Alkalin wata kotun majistare ya bukaci da a adana masa kakakin jam'iyyar PDP na jihar Gombe a gidan gyaran hali, bayan zarginsa da ake yi da caccakar jam'iyyar APC mai mulki.

Kakakin jam'iyyar PDP na karamar hukumar Gombe da ke jihar Gombe mai suna Khalid Mu'azu Izala, ya shiga hannun 'yan sanda kuma sun garkamesa a ofishinsu tun a ranar Juma'ar da ta gabata.

Hakan ya biyo bayan korafin wani mutum mai suna Garba Mohammed Mairago, wanda ya zargesa da yin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook a 2019, inda ya rubuta kalaman batanci a kansa tare da wasu 'yan jam'iyyar APC a jihar.

Kamar yadda rahoton farko na 'yan sandan ya bayyana kuma aka karanta a gaban kotun a ranar Talata, ya wallafa cewa Garba Mairago da wasu 'yan jam'iyyar APC na jihar Gomben na yunkurin kai masa hari.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sajan Peter, ya ce wanda ake zargin an gurfanar da shi a gaban kotun ne a kan laifi daya wanda shine bata suna. Hakan ya ci karo da sashi na 391 na dokokin Penal Code.

Kotu ta garkame kakakin jam'iyyar PDP a kan kalubalantar gwamnatin APC
Kotu ta garkame kakakin jam'iyyar PDP a kan kalubalantar gwamnatin APC. Hoto daga Daily Trust
Source: Facebook

KU KARANTA: Jerin jiga-jigan APC da ke zawarcin shugabancin jam'iyyar da manyan mukamai

A yayin da kotun ta tambaya Khalid Izala ko abinda 'yan sandan suka karanto gaskiya ne, ya musanta hakan.

A don haka, lauyoyin wanda ake kara, Barista Habu Audu da Benjamin Sati suka mika bukatar belin wanda suke karewa.

Amma kuma, sajan Peter ya soki bukatar belin kuma ya sanar da kotun cewa, akwai yuwuwar wanda ake zargin ya tsallake sharuddan belin ko kuma ya zama babbar barazana ga binciken 'yan sandan idan aka sakesa.

Alkalin kotun, Mai shari'a Bello Shariff, ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Satumba domin duba bukatar belin, tare da bada umarnin adana masa Izala a gidan gyaran hali na jihar Gombe.

An gano cewa, wanda ake zargin na tsare ne sakamakon wallafe-wallafensa na Facebook, inda yake kalubalantar wasu sabbin tsari da shirin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.

Idan za mu tuna, a watan Fabrairun da ta gabata wasu 'yan PDP biyu na jihar aka garkamesu a gidan yari a kan zagin Gwamna Yahaya Inuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel