Babu sanatan da ya karbi N20m na tallafin korona daga NDDC – Majalisar dattawa

Babu sanatan da ya karbi N20m na tallafin korona daga NDDC – Majalisar dattawa

Majalisar dattawa a ranar Talata, 1 ga watan Satumba, ta bayyana cewa mambobinta basu karbi naira miliyan 20 na tallafin korona daga hukumar ci gaban Neja Delta ba.

Daraktan ayyuka na kwamitin rikon kwarya na NDDC, Dr Cairo Ojougboh, ya yi zargi a hira da ya yi da wata jarida a kwanan nan cewa hukumar ta bai wa ýan majalisa kudi.

Ya yi ikirarin cewa kowani sanata ya samu naira miliyan 20 yayinda ta ba kowani dan majalisar wakilai naira miliyan 15 a matsayin tallafi.

Amma kakakin majalisar dattawa, Dr. Ajibola Basiru, ya karyata ikirarin Ojougboh a wani jawabi mai taken: “Shugaban NDDC ya ce sanatoci sun karbi N20m, yan majalisar wakilai sun karbi N15m kowannensu don COVID-19 – nesanta kai daga ikirarin."

Babu sanatan da ya karbi N20m na tallafin korona daga NDDC – Majalisar dattawa
Babu sanatan da ya karbi N20m na tallafin korona daga NDDC – Majalisar dattawa
Asali: Twitter

Basiru ya kalubalanci Ojougboh da ya saki cikakken sunayen ‘yan majalisar da suka amfana daga tallafin ko kuma ya fito bainar jama’a ya bayar da hakuri ba tare da bata lokaci ba.

KU KARANTA KUMA: Wani malamin coci ya yanke jiki ya mutu yana tsakiyar ibada a coci

Sanata Ajibola Basiru ya ce: "Majalisa ta karyata cewa babu wani sanata da ya karbi naira miliyan 20 ko wani kudi daga hukumar NDDC a matsayin tallafin korona ko kuma wani dalili.

"Majalisa ta kalubalanci Dr Ojougboh ya kawo hujjar zargin da ya yi ta hanyar wallafa sunayen sanatocin.

"Idan ya gaza yin hakan, Majalisa na bukatar ya yi gaggawan janye maganar sannan ya nemi afuwar jama'a."

A baya mun ji cewa Cairo, ya ce Najeriya zata tarwatse idan har hukumar ta saki jerin sunayen manyan kasar da suka amfana daga ayyukan kwangiloli da hukumar ta bayar.

Kallo ya koma kan hukumar NDDC bayan majalisar dokokin tarayya ta kaddamar da bincike kan zargin badakalar kudade a hukumar.

Binciken ya dauki sabon salo lokacin da ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya zargi ýan majalisar tarayya da daukar babban kaso a kwangilolin da hukumar ta rabar.

Har da Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan NDDC, cikin wadanda ministan ya ce sun amfana da kwangilolin.

Sauran sune Peter Nwaoboshi, Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan asusu, Matthew Urhoghide da sanata mai wakiltan Delta ta Kudu, James Manager.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel