Da duminsa: Obaseki, Ize-Iyamu da Oshiomhole sun shiga ganawar gaggawa

Da duminsa: Obaseki, Ize-Iyamu da Oshiomhole sun shiga ganawar gaggawa

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP; abokin hamayyarsa Pastor Osagie Ize-Iyamu da tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole sun shiga ganawa, don yin sulhu, bisa jagorancin Sarkin Benin.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Omo ‘N’Oba N’Edo Uku Akpolokpolo, Oba Ewuare 11, ya jagoranci ganawar ne domin tattaunawa tsakanin kusoshin zaben gwamnan jihar.

A ranar 19 ga watan Satumba 2020 ne hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta shirya gudanar da zaben jihar Edo.

Rahotanni sun bayyana cewa sauran 'yan takara daga jam'iyyun siyasar kasar sun halarci taron.

Cikakken labarin yana zuwa...

KARANTA WANNAN: Jaridar Charlie Hebdo ta sake buga hotunan batanci ga Annabi Muhammadu (SAW)

Da duminsa: Obaseki, Ize-Iyamu da Oshiomhole sun shiga ganawar gaggawa
Da duminsa: Obaseki, Ize-Iyamu da Oshiomhole sun shiga ganawar gaggawa
Source: Twitter

A wani labarin, jaridar Charlie Hebdo, ta sake wallafa hotunan barkwancin da suka yi shekaru 5 da suka wuce, na batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

A 2015, jaridar wacce tayi kaurin suna wajen yin zane zanen barkwanci, ta zana siffar Annabi, lamarin da ya fusata kungiyar wasu Musulmai, har suka kai mata hari.

A shekarar 2005 ne jaridar Jyllands-Posten ta fara wallafa zanen.

Sake wallafa zanen na zuwa ne kwana ɗaya kafin soma shari'ar mutanen nan 14 da ake zargi da taimaka wa wasu mutum biyu masu iƙirarin jihadi da kai harin bindiga a ofishin mujallar a ranar 7 ga watan Janairun 2015.

A wannan karon, shugaban dab'i na jaridar, Laurent "Riss" Sourisseau ya ce ba za su ja da baya ba, kuma tuni sun saki hotunan a yanar gizo, ba zasu wallafa a jaridu ba.

Riss ya rasa hannunsa na dama a harin da aka kaiwa jaridar a ranar 7 ga watan Janairu, sai dai ya rayu ne bayan da ya yi lambo kamar ya mutu a lokacin.

Hotunan barkwancin da suka zana akan Annabi Muhammadu, sun zamo abun batanci da cin zarafi, wanda ya sa har kungiyar Said da Cherif Kouachi suka farmaki ginin jaridar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel