'Yan majalisa sun karbi N20m, N15m a matsayin tallafin korona - Darektan NDDC

'Yan majalisa sun karbi N20m, N15m a matsayin tallafin korona - Darektan NDDC

- Dakta Cairo Ojougboh, darektan aiyuka a hukumar kula da cigaban yankin Neja-Delta, ya ce sun rabawa mambobin majalisa tallafin rage radadin annobar korona

- Majalisar dattiai ta musanta zargin Dakta Ojougboh tare da neman ya gabatar da wata hujja ko kuma ya bayyana sunayen mambobin da suka karbi tallafin

- Tun bayan fara gudanar da binciken badakala a hukumar NDDC ake ta bankado almundahana kala-kala da manyan jami'an gwamnati da 'yan majalisa suka tafka

Babban darektan aiyuka a hukumar kula da cigaban yankin Neja-Delta (NDDC), Cairo Ojougboh, ya yi zargin cewa sun bawa mambobin majalisar tarayya tallafin annobar cutar korona.

Yayin wata hirarsa da jaridar vanguard, Ojougboh ya yi zargin cewa kowanne mamba a majalisar dattijai ya karbi N20m, yayin da kowanne mamba a majalisar wakilai ya karbi N15m daga hukumar NDDC a matsayin tallafin cutar korona.

Sai dai, majalisar dattijai ta yi watsi da zargin cewa mambobinta sun karbi miliyan N20 daga hukumar NDDC a matsayin tallafin cutar korona.

Da ya ke musanta hakan ranar Talata, kakakin majalisar dattijai, Dakta Ajibola Basiru, ya kalubalanci babban darektan NDDC ya wallafa shaidar da zai tabbatar da zargin da ya furta ta hanyar "fitar da sunayen dukkan sanatocin da ya yi zargin cewa sun karbi tallafin".

'Yan majalisa sun karbi N20m, N15m a matsayin tallafin korona - Darektan NDDC
Majalisar dattijai
Source: Facebook

"Hankalin majalisar dattijai ya kai kan wani rahoto da aka alakanta da Dakta Cairo Ojougbo, babban darektan aiyuka na NDDC, inda ya yi zargin cewa mambobin majalisa sun karbi makudan kudade a matsayin tallafin rage radadin annobar korona.

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya shawarci Buhari ya wakilta wasu dattijai hudu da za su warware matsalar rashin tsaro a arewa

"Majalisar dattijai ta musanta gaba daya wannan zargi. Majalisar dattijai ta musanta, da manyan haruffa, cewa babu wani sanata da ya karbi miliyan N20 ko wani dadin kudi daga hukumar NDDC a matsayin tallafin korona ko kuma saboda wani dalili.

"Mun kalubalanci Dakta Ojougboh ya wallafa wata shaida, musamman sunyayen mambobin da ya yi zargin cewa an bawa adadin kudaden.

"Matukar kuma ba zai iya yin hakan ba, majalisar dattijai ta na bukatar ya janye kalamansa tare da wallafa takardar neman afuwa mai dauke da sunansa da sa hannunsa," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel