Shehu Sani ya shawarci Buhari ya wakilta wasu dattijai hudu da za su warware matsalar rashin tsaro a arewa

Shehu Sani ya shawarci Buhari ya wakilta wasu dattijai hudu da za su warware matsalar rashin tsaro a arewa

- Jihohin arewa da dama sun tsinci kansu a cikin matsalolin rashin tsaro a 'yan shekarun baya bayan nan

- Tsohon sanata, Kwamred Shehu Sani, ya shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa kwamiti domin dawo da zaman lafiya a yankin arewa

- Shehu Sani ya shawarci Buhari ya saka Yakubu Gowon, Abdulsalami Abubakar, Farfesa Jubril Aminu, da Audu Ogbeh, a matsayin jagororin kwamitin

Kwamred Shehu Sani, tsohon sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, ya shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa kwamitin da zai warware matsalolin kabilanci da rigingimu saboda banbancin addini ko darika a yankin arewa.

Da ya ke bayar da wannan shawara a ranar Litinin, Shehu Sani ya ce kwamitin ya kamata ya kunshi Yakubu Gowon, Abdulsalami Abubakar, Jubril Aminu, da Audu Ogbeh, a matsayin jagorori.

Tsohon Sanatan ya bukaci shugaba Buhari ya mayar da hankali a kan warware matsalolin arewacin Najeriya, sannan ya kara da cewa; "yankin kudu ba ya fuskantar kalubalen tsaro saboda matsalolin banbancin addini ko darika.

"Ya kamata shugaba Buhari ya wakilta Janar Gowon, Abdulsalami Abubakar, Audu Ogbeh, da Farfesa Jubril Aminu domin su bullo da sabbin hanyoyin kawo karshen rigingimu ma su nasaba da kabilanci da banbacin addini da kuma rikicin manoma da makiya domin dawo da zaman lafiya a yankin arewa," kamar yadda Sanata Sani ya rubuta a shafinsa na tuwita.

Shehu Sani ya shawarci Buhari ya wakilta wasu dattijai biyu da za su warware matsalar rashin tsaro a arewa
Shehu Sani da Buhari
Source: UGC

Sanna ya kara da cewa; "yankin kudancin Najeriya ba ya fuskantar kalubalen tsaro saboda matsalolin banbancin addini ko darika."

DUBA WANNAN: Ma su garkuwa da mutane sun tare babbar hanya a Kano, kwamandan HISBAH ya sha da kyar

A 'yan shekaru baya bayan nan, jihohin arewa da dama sun tsinci kansu a cikin matsalolin rashin tsaro da suka hada da rikicin manoma da makiyaya, barnar dukiya da rayuka da 'yan bindiga ke yi, garkuwa da mutane da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel