NAF za ta tura jirgin yaki Edo a yayinda ake tsaka da kamfen din zabe a jihar

NAF za ta tura jirgin yaki Edo a yayinda ake tsaka da kamfen din zabe a jihar

- Rundunar sojin saman Najeriya za ta tura Jirgin yaki jihar Edo domin tabbatar da tsaro gabannin zaben gwamna

- Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Benin

- Ya ce tura sabon jirgin yaki zuwa jihar Edo domin bunkasa yaki da ta’addanci da kuma tabbatar da tsaron yankin kasar

Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce za a tura sabon jirgin yaki zuwa jihar Edo domin bunkasa yaki da ta’addanci da kuma tabbatar da tsaron yankin tekun na kasar.

Sanarwar na zuwa ne yayinda jam’iyyun siyasa ke tsaka da kamfen gabannin zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 19 ga watan Satumba.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta nuna damuwa kan yiwuwar barkewar rikici a lokacin zaben.

Yayinda yake ziyarar gani da ido a wasu gine-gine a birnin Benin, a ranar Juma’a, Abubakar ya yaba ma jami’an rundunar sojin saman Najeriya reshen jihar Edo a kan gudunmawarsu ga tsaron kasa.

NAF za ta tura jirgin yaki Edo a yayinda ake tsaka da kamfen din zabe a jihar
NAF za ta tura jirgin yaki Edo a yayinda ake tsaka da kamfen din zabe a jihar Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Jirgin aiki na musamman zai karfafa tsaron yankin tekun na Najeriya kuma na yarda wannan sashi zai taka muhimmin rawa wajen tabbatar da cewar sashin tekun ya samu tsaro,” in ji shi.

Abubakar ya bayyana cewa koda dai akwai rumfar ajiye jiragen sama a Benin, akwai bukatar jirgin yaki da wasu kayayyakin tallafi domin ganin sabon jirgin ya yi aiki yadda ya kamata.

Ya kara da cewa: “za a tura matukan jirgi, masu gyara da jami’ai injiniyoyi zuwa Benin da kuma rundunar sojin sama na musamman. Baya ga sauran kayayyaki, za a samar masu da gida da ofis.”

KU KARANTA KUMA: Sarkin Oyo ya bayyana yadda aka yi ya tara mata da yawa

A halin da ake ciki, shugaban kungiyar kamfen na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Edo, Cif Dan Orbih, a ranar Asabar ya ce zabe mai zuwa zai kawo karshen ubangida a jihar.

Hakan na zuwa ne a yayinda kungiyar masu ra’ayin mazan jiya na Edo ta tsakiya ta ce ta mara wa dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Fasto Osagie Ize-Iyamu baya, jaridar Punch ta ruwaito.

Orbih, a wani jawabi, ya bukaci masu zabe da su fito kwansu da kwarkwatarsu don tabbatar da sake zabar Gwamna Godwin Obaseki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng