Kwallon kafa: Jerin Kungiyoyin da za su iya ba ‘Yan wasa ciwon kai a badi

Kwallon kafa: Jerin Kungiyoyin da za su iya ba ‘Yan wasa ciwon kai a badi

Kungiyar Bayern Munich ce ta lashe gasar zakarun nahiyar Turai na shekarar bana. Kungiyar ta doke irinsu Tottenham, Chelsea, Barcelona a kan hanya.

Wannan ne karo na shida da kungiyar ta kasar Jamus ta yi nasara a Turai. Karon karshe da Bayern ta lashe wannan kofi shi ne a 2013 karkashin Jupp Heynckes.

Legit.ng Hausa ta kawo maku jerin kungiyoyin da ake tunanin za su fafata wajen karbe wannan kofi daga hannun Bayern Munich a gasar shekara mai zuwa.

1. PSG

Kungiyar PSG ce ta isa wasan karshe tare da Bayern Munich, amma ba ta yi nasara ba. A 2021 ana tunanin Neymar Jr., Angel Di Maria da irinsu Kylian Mbappe za su kara kokari.

2. Manchester City

Man City za ta nemi yin abin kwarai a shekara mai zuwa musamman yadda nauyi ke kara hawa kan kocin kungiyar, Pep Guardiola wanda aka yi wa cafane yadda zai yi nasara.

3. Barcelona

A Sifen, Barelona ta na cikin zakaru a Turai, sai dai kungiyar ta yi shekaru rabonta da nasara.

KU KARANTA: Sai Messi ya biya $800m sannan zai iya barin Barcelona

Kwallon kafa: Jerin Kungiyoyin da za su iya ba ‘Yan wasa ciwon kai a badi
Zinedine Zidane zai kalubalanci Hansi Flick
Asali: UGC

Akwai yiwuwar Barcelona ta dage a shekarar badi musamman idan ta hana Lionel Messi tashi.

4. Liverpool

Wata kungiyar Firimiya da za ta iya kawowa Bayern Munich cikas ita ce Liverpool. Zakarun na Ingila su ne su ka yi nasarar lashe wannan gasa a 2019 a karawarsu da Tottenham a Madrid.

5. Juventus

A 2021, ba za a cire Juventus daga lissafin wadanda za su tabuka abin kwarai ba. An shafe shekara da shekaru rabon da Juventus ta yi nasara, sai dai yanzu ta na da Cristiano Ronaldo.

6. Real Madrid

Real Madrid ba sababbin shiga ba ne a wannan sahu, kungiyar ta saba samun nasara a Turai. Zinedine Zidane ya dauki shekaru a jere ya na lashe wannan kofi, a saurare shi a 2021.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng