Barayi sun sace mai jego kwana hudu bayan ta haihu a jihar Taraba

Barayi sun sace mai jego kwana hudu bayan ta haihu a jihar Taraba

- Barayi sun sace wata mata mai jego da tsakar dare kwanaki hudu bayan ta haihu

- An ruwaito cewa barayin sun je neman mijinta ne, inda shi kuma ya samu ya gudu daga gidan kafin su isa wajen shi

- Sai dai sun bar jaririnda ta haifa basu tafi dashi ba, duk kuwa da ta bukaci ta tafi da danta

Wasu mutane da ake zargin barayi ne sun sace wata matar aure a kauyen Namne dake cikin karamar hukumar Gassol dake jihar Taraba a ranar Asabar, kwanaki hudu kacal da ta haihu.

Matar mai suna Zainab Buba, mai shekaru 25, an ruwaito cewa ta haifi yaro namiji kwanaki hudu da suka wuce, inda kuma da tsakar dare aka sace ta.

Barayi sun sace mai jego kwana hudu bayan ta haihu a jihar Taraba
Barayi sun sace mai jego kwana hudu bayan ta haihu a jihar Taraba
Source: Facebook

Barayin sun bar jaririn basu tafi da shi ba, duk da kuwa mahaifiyar jaririn ta nemi ta tafi da jaririnta.

Daily Trust ta gano cewa mijin Zainab, Buba Mai Unguwa, mutum ne da yake da mukamin gargajiya.

An ruwaito cewa 'yan bindigar sun nemi Buba ne wanda yake da garken shanu, amma ya samu ya gudu daga bayan gidan a lokacin da suka shiga gidan nashi.

KU KARANTA: Wani mutumi ya yiwa karamar yarinya fyade a lokacin da taje kogi wankin kaya

Mutanen yankin sun bazama neman mai jegon wacce jaririnta ke ta faman kuka, yayin da aka bawa wata mata mai jego ta lura da shi a cikin kauyen.

Daily Trust ta gano cewa barayin sun kira Buba Mai Unguwa, wanda yake shine miji ga zainab, inda suka bukaci ya biya kudin fansa.

Yayin da aka yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar DSP David Misal, abin yaci tura, inda wayarshi aka same ta a kashe a yayin da wakilin Daily Trust ya tuntube shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel