Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun halaka kansilan PDP mai ci

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun halaka kansilan PDP mai ci

- 'Yan bindiga sun halaka kansila a karamar hukumar Sagamu ta jihar Bayelsa

- An gano cewa yana dawowa ne daga wani gagarumin taron jam'iyyar PDP da aka yi a yankin

- Ganau ba jiyau ba, ya tabbatar da cewa asibitoci biyu sun ki karbarsa sai da 'yan sanda, lamarin da ya kawo ajalinsa

Karma Agagowei kansila ne mai wakiltar gunduma ta 6 a karamar hukumar Sagamu ta jihar Bayelsa.

A cikin ranakun karshen makon nan, 'yan bindiga suka kutsa yankin Opolo da ke wani sashi na babban birnin jihar inda suka kasheshi

An gano cewa yana dawowa ne daga wani gagarumin taron jam'iyyarsa ta PDP da aka yi a yankin, jaridar Vanguard ta wallafa.

An gaggauta mika kansilan asibitoci har biyu daban-daban, wadanda suka hada da Gloryland da FMC Yenagoa, amma an ki karbarsa.

Ma'aikatan lafiyan sun bukaci samun 'yan sanda kafin su taba kansilan, amma kuma kafin nan yace ga garinku.

Wani ganau ba jiyau ba, ya ce marigayin na cikin adaidaita sahu yayin da lamarin ya faru.

Sun tsaresu da adduna inda suka ji masa raunika masu tarin yawa sannan suka tsere.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Anisim Butswat, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani ba.

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun halaka shugaban karamar hukuma mai ci
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun halaka shugaban karamar hukuma mai ci. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Lauyan da yayi murnar mutuwar Kyari da Funtua, da fatan mutuwar Buhari ya rasu

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Talata ya ziyarci Magumeri, hedkwatar karamar hukumar Magumeri ta jiharsa bayan harin 'yan Boko Haram.

Gwamnan ya yi jawabi ga mazauna yankin, kuma ya duba yanayin barnar da mayakan ta'addancin suka yi a asibitin Magumeri da ba a dade da gyarawa ba.

A sakon Zulum ga mazauna yankin yayin jawabinsa, ya yi kira ga mazauna yakin da su kai rahoton duk wani mutum ko kaiwa da kawowa da basu yadda da ita ba ga jami'an tsaro don kawo karshen duk wani nau'in ta'addanci.

"Akwai matukar amfani idan mazauna yankin suka bai wa jami'an tsaro goyon baya ta hanyar samar musu da bayanan sirri, don samun hanyar damko 'yan ta'addan da masu goyon bayansu.

"Bayanai daga jama'ar yankin na da matukar amfani. Baya ga karfafa CJTF, gwamnati na kira ga jama'ar yankin da su samar da bayanai ga dakarun sojin da sauran hukumomin tsaro," Zulum yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: