Jahilai ne masu ruwa da tsaki a kasuwancin magunguna a Kano - PCN

Jahilai ne masu ruwa da tsaki a kasuwancin magunguna a Kano - PCN

Kungiyar masu harhada magunguna ta Najeriya (PCN) ta ce marasa ilimi sun fi yawa a sana’ar harhada magunguna a jihar Kano, wadanda tace suna jefa rayukan mutane da ke zuwa a basu magani cikin hatsari.

Kungiyar PCN ta ce ta gano hakan ne bayan wani shirin gani da ido da ta gudanar a mafi akasarin kananan hukumomi a Jihar Kano, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Misis Anthonia Aruya, wata daraktan PCN ta fada ma manema labarai cewa kungiyar ta ziyarci wajen harhada magunguna 65 da shagunan PPMV 931 a cikin kwanaki uku.

Sannan ta ce sun gano cewa mafi akasarin shagunan magunguna mallakar mutanen da basu da kwarewa ne, wadanda ke aiki ba tare da kowani ilimi ba.

KU KARANTA KUMA: Zamfara za ta fara yankewa masu tukin ganganci hukuncin kisa bayan mutuwar wasu magoya bayan gwamnan su

Jahilai ne masu ruwa da tsaki a kasuwancin magunguna a Kano - PCN
Jahilai ne masu ruwa da tsaki a kasuwancin magunguna a Kano - PCN
Source: UGC

Ta ce kungiyar ta rufe wuri 677 da suka hada da manyan kantunan sayar da magunguna 41, da kananan shaguna 636 wadanda basu da rijista ko rashin sabonta lasisinsu kamar yadda dokar PCN ta tanadar.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Fadila mutuniyar kirki ce a lokacin da take tashe – Falalu Dorayi

An bayar da umurni 15 ga wasu masu hada magunguna uku da PPMV 12 kan “wasu baraka.”

Ta ce: “An gano daga binciken cewa masu wasu masu ruwa da tsaki da dama sun bude manyan kantin siyar da magunguna ba tare da bin ka’ida ba. Wasun su basu iya rubutu ko karatun turanci ba wanda hakan ya sa muke mamakin ta yadda suke iya bayar da umurnin da ya dace kan yadda mara lafiya zai yi amfani da magani.

"Gaba daya, akwai rashin fahimtar gaskiyar cewa lamarin hada magani aiki ne da akwai masu iliminsa na musamman wato kwararru kafin ma mutum ya yi tunanin daukarsa a matsayin sana’a.

"Kungiyar PCN za ta bi tsarin da ya kamata wajen wayar da kai domin inganta yanayin aikinta a jihar Kano. Wadanda abun ya shafa za a musu gyara sannan a daura su kan matakan da ya kamata kuma za a kyale wadanda ke da abubuwan da ake bukata ci gaba da sana’arsu ta hada magunguna,” in ji Aruya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel