Yan Boko Haram sun kashe manoma biyu, sun yi garkuwa da biyu

Yan Boko Haram sun kashe manoma biyu, sun yi garkuwa da biyu

Mayakan Boko Haram a kan dawakai sun kashe mutum biyu tare da sace wasu biyun a yayin da suka kaiwa wasu manoma hari a wajen Maiduguri da ke yankin arewa maso gabas a Najeriya, AFP ta sanar.

A ranar Juma'a 'yan ta'addan suka shiga wasu gonaki da ke kauyen Alau inda suma sace manoma hudu. A take suka kashe biyu daga ciki sannan suka yi awon gaba da biyu. Sun ji wa wasu raunika kafin su tsere, wasu majiyoyi suka sanar.

"Mun samu gawawwakin manoma biyu tare da miyagun raunika a cikinsu," Mohammed Bukar yace.

"Manoman da suka tsere sun ce an raunata wasu kuma an yi garkuwa da biyu daga ciki," Bukar ya kara da cewa.

Yan Boko Haram sun kashe mutum biyu, sun yi garkuwa da biyu
Yan Boko Haram sun kashe mutum biyu, sun yi garkuwa da biyu. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

Manoman mazauna wani sansanin 'yan gudun hijira a wajen birnin suna noma a kauyen ne, shugaban kungiyar mazauna yankin Babakura Kolo ya sanar.

A kalla mutum miliyan biyu ne suka rasa gidajensu bayan sama da shekaru goma da yankin ya kwashe babu zaman lafiya. Da yawa daga cikin jama'ar suna zama a sansanin 'yan gudun hijira inda suka dogara da tallafin kungiyoyin jin kai don taimako.

Wasu daga cikinsu sun koma yin itace inda suke siyar da itacen don samun kudin amfani. Wasu kuwa sun koma noma a gonakin da ke da kusanci da su.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Jirgi mai saukar ungulu ya afka wa wani gini a Legas

Mayakan ta'addancin Boko Haram sun koma kai wa manoma, makiyaya da masunta hari bayan zarginsu da suke yi da kai wa jami'an tsaro bayanan sirri game da su.

Rikicin Boko Haram ya fara yankin arewa maso gabas na kasar nan a 2009, kuma a kalla rayuka 36,000 ala rasa yayin da mutum miliyan biyu suka rasa gidajensu.

Tuni rikicin ya shafi kasashe masu makwabtaka da Najeriya irinsu Nijar, Chadi da Kamaru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel