Mutum uku sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a jihar Adamawa

Mutum uku sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a jihar Adamawa

Rahotanni sun kawo cewa wasu mutum uku da aka bayyana a matsayin Melody M, Isaac G., da James S., sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a jihar Adamawa.

Shafin Linda Ikeji ya ruwaito cewa mutanen, wadanda suka kasance maza biyu da mace guda, sun nitse ne a yayinda suke a hanyarsu ta zuwa bikin binne wani a karamar hukumar Lamurde bayan kwale-kwalen ya kife.

Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban karamar hukumar Lamurde, Burto Williams, ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki.

KU KARANTA KUMA: Rikici ya barke a kasar Sweden sakamakon shirya taron kona Al-Kur'ani da wasu sukayi

Mutum uku sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a jihar Adamawa
Mutum uku sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a jihar Adamawa
Source: UGC

“Hatsarin abun bakin ciki ne da yake bukatar gwamnati ta kawo agaji ga mutanen yankin wadanda ruwa ke yawan yi wa barna.

“Karamar hukumar Lamurde na kokarin samar da kulawar likitoci ga wadanda suka tsira yayinda hukumar za ta dauki nauyin birne mutum uku da suka mutu,” in ji Burto.

KU KARANTA KUMA: FG ta ce ba za ta kara lamuntan cin zarafin ‘yan Najeriya a Ghana ba

A wani labari na daban, mun ji cewa mutane biyar sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta debe dubban gidaje da gonaki a karamar hukumar Goronyo da ke jihar Sokoto.

Daily Trust ta gano cewa, ambaliyar ruwan ta hada da dabbobin da ake kiwo tare da hatsi.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, shugaban yankin, Zakari Muhammad Shinaka ya ce sama da gidaje 2000 ne suka salwanta a garin Rimawa kadai.

Ya kara da cewa, gidaje masu tarin yawa da gonaki sun salwanta a Katsira, Kagara, Gorau, Birjingo, Shinaka da wani bangare na Sabon Garin Dole.

Sauran wuraren da ambaliyar ruwan ta shafa ya hada da Rimawa, Tulaske, Kwakwaza, Ilela Huda da Danwaru tare da sauran wuraren da ke da kusanci da ruwa.

Daga cikin amfanin gonar da ambaliyar ruwan ya tafi da su sun hada da shinkafa, dawa, gero da masara.

Ya yi bayanin cewa, wani tsoho da 'ya'yansa biyu sun rasa rayukansu sakamakon faduwar gini a Gebe. Wasu karin mutum biyu sun rasu sakamakon ibtila'in a kauyen Giyawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel