Kwamitin da ke binciken Magu ya fara binciken wani toshon IGP, an kwace wasu gidajensa

Kwamitin da ke binciken Magu ya fara binciken wani toshon IGP, an kwace wasu gidajensa

Kwamitin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa a karkashin jagorancin Jastis Isa Ayo Salami ya sake bude fayil din binciken tsohon babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Tafa Balogun, wanda aka taba gurfanarwa da laifin cin hanci a shekarar 2005.

Shugaba Buhari ya kafa kwamitin ne domin gudanar da bincike tare da kwato kadarorin gwamnati daga hannun wasu manyan jami'an gwamnati; na baya da na yanzu, da ake zargi da almundahana, waskiya, ko sama da fadi da dukiya ko kadarar gwamnati.

Har yanzu kwamitin ya na cigaba da gudanar da bincike a kan shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) da Buhari ya dakatar, wato Ibrahim Magu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa kwamitin ya gayyaci Mista Francis Ajala, mutumin da EFCC ke nema ruwa a jallo saboda gudunmawar da ya bawa tsohon IGP Tafa Balogun wajen tafka almundahana.

Punch ta rawaito cewa kwamitin ya gayyaci Mista Ajala ne domin ya yi bayani a kan rawar da ya taka wajen karkatar da wasu kudade da ake zargin Tafa Balogun ya wawuresu a lokacin da ya ke IGP.

Zai bayar da bayani ne a matsayinsa na tsohon mataimakin babban manaja a tsohon bankin Fountain Trust Bank reshen Abuja.

Kwamitin da ke binciken Magu ya fara binciken wani toshon IGP, an kwace wasu gidajensa
Jastis Isa Ayo Salami
Asali: UGC

Wata majiya daga cikin kwamitin ta sanar da Punch cewa Mista Ajala ya sanar da kwamitin cewa shine ya mallaki wasu daga cikin gidajen da EFCC ta kwace bisa tsammanin na Tafa Balogun ne.

"Kwamiti ya gayyaci Mista Ajala, mutumin da EFCC ta bayyana cewa tana nema ruwa a jallo tun shekarar 2008 kuma har yanzu ba a wanke shi daga zargin da ake masa ba.

DUBA WANNAN: Farfesa Wole Soyinka ya caccaki shugaba Buhari a kan shirin kirkirar wata sabuwar doka a Najeriya

"Mista Ajala ya sanar da kwamiti cewa shine ya mallaki wasu daga cikin gidajen da aka kwace a Ikoyi da Victoria Island bisa tsammanin cewar mallakar Tafa Balogun ne," a cewar majiyar Punch

A cewar Punch, kwamitin da Salami ke jagoranta ya fara gudanar da bincike a kan wasu daga cikin manyan laifuka da Magu ya jagoranci bincikensu tun daga shekarar 2004.

Magu ya taka muhimmiyar rawa wajen bincike, gurfanarwa tare da kwace kadarorin Tafa Balogun a lokacin ya na aiki da sashen gudanar da aiyuka na hukumar EFCC.

Daga cikin gidajen da aka kwace daga hannun Tafa Balogun akwai rukunin wasu gidaje shidda ma su dakunan kwana uku a unguwar Ikoyi, wani gida mai dakin kwana biyar a Victoria Garden City dake unguwar Ajah, wani katon gida mai sassa daban-daban a unguwar Ikoyi, duk a jihar Legas.

Ragowar sun hada da wani gida a titin Suez Crescent da ke unguwar Wuse Zone 4, rukunin wasu gidaje biyar a Tunis Street da ke ungwar Wuse Zone 6, da kuma wani babban gida a kan titin Mamman Nasir da ke unguwar Asokoro, duk a Abuja.

Da ya ke tabbatar da hakan, lauyan Magu, Mista Tosin Ojaomo, ya ce a bayyane take cewa kwamitin neman laifukan Magu ya ke yi ido rufe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel