Gwamnatin Tarayya ta na tsarin biyan Malaman makarantun kudi – Osinbajo

Gwamnatin Tarayya ta na tsarin biyan Malaman makarantun kudi – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta na kokarin ganin ta taimakawa malaman makarantar da su ke cikin matsala.

A ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, aka ji Yemi Osinbajo ya na cewa su na tsara inda za a tattara sunayen malaman makarantun kudi da su ka daina samun albashi.

A dalilin annobar COVID-19 da ta jefa tattalin arzikin kasashen Duniya cikin matsala, malaman makarantun kudi a Najeriya ba su zuwa aiki, kuma ba su samun albashi.

Mataimakin shugaban Najeriyar ya ce gwamnatinsu ta kama hanyar kawo yadda za ta tallafawa wadannan malamai domin a rage radadin da annobar ta jefa Bayin Allah.

Bayan malaman makarantu, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya za ta kawowa masu aikin hannu dauki, wadanda su ma sun shiga cikin halin ha’ula’i.

Osinbajo ya bayyana haka ne a wajen taron kungiyar lauyoyi na kasa watau NBA da aka yi jiya.

KU KARANTA: Za a karbe kwangila idan ba a kammala aikin Kaduna - Abuja a 2021 ba

Gwamnatin Tarayya ta na tsarin biyan Malaman makarantun kudi – Osinbajo
Osinbajo ya fadi shirin Gwamnatin Buhari
Asali: Twitter

An zabi mataimakin shugaban Najeriyar ya yi jawabi ne game da halin da kasa ta ke ciki, wanda ya zama shugaban wannan zama shi ne Mista Nduka Obaigbena.

A jawabinsa, mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnati ta samu filaye a jihohi 11 da ke fadin kasar nan, inda za ta ginawa mutane kananan gidaje mai cin daki biyu.

Kamar yadda Farfesa Osinbajo ya bayyana, za a gina wadannan gidaje ne a kan Naira miliyan biyu. Wannan zai taimaka wajen rage karancin wurin zama da samar da abin yi.

Osinbajo ya ce kokarin gwamnatin Muhammadu Buhari shi ne ganin sun ceto aikin mutane, tare da samar da wasu hanyoyin abin yin a lokacin wannan annoba.

“Mu na tattara bayanan nan, mun bayyana sharudan da za ayi amfani da shi. Akwai shirin da ake yi na taimakawa masu harkar otel da aikin jiragen sama.” Inji Osinbajo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel