Da duminsa: Shugaba Buhari ya halarci taron ECOWAS kan rikicin Mali
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya goyi bayan ECOWAS na bawa sojojin kasar Mali wa'adin wata 12 domin su mika mulki zuwa ga farar hula.
A yau, Juma'a, ne shugaba Buhari ya halarci taro na biyu ta yanar gizo na shuwagabannin kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS dangane da rikicin da ke faruwa a Mali.
Dukkannin shuwagabannin kasashen ECOWAS sun halarci taron, bisa jagorancin shugaban kungiyar ta ECOWAS, Jean-Claude Kassi Brou.
Ana sa ran batutuwan da za a tattauna a taron ya kasance kan hanyoyin da za a kawo karshen rikicin siyasa da ya mamaye kasar ta Mali.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanar daga mai baiwa shugaban kasar shawara kan kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad, da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A karshen watannan ne dai wasu sojojin hamayya suka hambarar da gwamnatin shugaban kasa Ibrahim Keita, lamarin da ya ja ECOWAS ta cire kasar daga cikin kungiyar.
Sojojin da suka yi juyin mulkin sun bukaci yin shugabanci na tsawon shekaru uku kafin su mika mulki a hannun farar hula.
Sai dai, ECOWAS ta bayyana cewa ya zama dole sojojin su mika mulki zuwa hannun farar hula a cikin watanni 12, watau shekara daya.
DUBA WANNAN: Farfesa Wole Soyinka ya caccaki shugaba Buhari a kan shirin kirkirar wata sabuwar doka a Najeriya
Wadanda suka halarci dakin taron da shugaba Buhari ke ganawa da shugabannin ECOWAS ta yanar gizo sun hada da ministocin harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyema, da Zubairu Dada.
Sauran sun hada da ministan tsaro; Bashir Magashi, shugaban ma'aikatan fada shugaban kasa; Farfesa Ibrahin Gambari, NSA; Babagana Monguno da shugaban hukumar NIA; Ahmed Rufa'i Abubakar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng