Yawan kudin da Messi yake dauka a kulob din Barcelona duk shekara

Yawan kudin da Messi yake dauka a kulob din Barcelona duk shekara

- Fitaccen dan wasa Lionel Messi zai bar kulob din Barcelona a wannan shekara, amma zai yi wahala wasu kulob din su iya biyanshi kudin da ake bashi a Barcelona

- Kulob din Ingila na Manchester City sune kulob din da suka nuna zasu sayi dan wasan mai shekaru 33

- Messi dai shine tauraro na biyar a duniya da yafi kowa daukar kudi banda Ronaldo, Federer, West da Jenner

Kokarin da Messi yake yi na barin kulob din Barcelona ba akan kudi bane, saboda fitaccen dan wasan na kasar Argentina ya tara kudin da zai iya ciyar da kanshi har karshen rayuwar shi.

Dan wasan mai shekaru 33 bai jin dadin abinda ke faruwa a kulob din bayan sun kasa samun nasarar cin kofin zakarun Turai da aka gabatar, inda kuma yake ganin lokaci yayi da zai bar kulob din.

Yawan kudin da Messi yake dauka a kulob din Barcelona duk shekara
Yawan kudin da Messi yake dauka a kulob din Barcelona duk shekara
Asali: UGC

Kulob din Manchester City sune kadai a yankin Turai da suka sanya kudin da zai iya daidai da albashin dan wasan, da kuma kudin da kulob din Barcelona ya gindaya dan sakin dan wasan.

KU KARANTA: Kana taka Allah na tashi: Matar aure da ta shafe shekara bakwai tana neman haihuwa ta mutu awanni kadan bayan ta haifi 'yan hudu

SunSport sun lissafa yawan kudin da Messi ya samu a Barcelona, don ganin ko kulob din Manchester City din zasu iya sayen shi.

Dan wasan na kasar Argentina a yanzu yana daukar albashin Fam miliyan 54, sannan kuma yana samun Fam miliyan 24 a kowacce shekara wajen tallace-tallace da daukar nauyi, kamar yadda Forbes ta ruwaito.

Haka kuma yana samun rarar kudi har Fam miliyan 13, inda yake samun Fam miliyan 81 a kowacce shekara, hakan ya sanya ya zama tauraro na biyar a duniya da yafi kowa daukar albashi mai yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel