Shekara mai zuwa a Juventus zan yi wasa – Ronaldo ya tabbatar da zamansa

Shekara mai zuwa a Juventus zan yi wasa – Ronaldo ya tabbatar da zamansa

- Cristiano Ronaldo ya yi watsi da rade-radin cewa zai tashi daga Juventus

- ‘Dan wasan mai shekaru 35 ya tabbatar cewa zai zauna Kungiyar Juventus

- Tauraron ya na sa ran ya yi aiki da Andrea Pirlo, ya cigaba da kafa tarihi

Cristiano Ronaldo ya yi magana game da inda zai taka leda a kaka mai zuwa, ‘dan wasan ya tabbatar da cewa bai da niyyar barin kungiyar Juventus a halin yanzu.

Shahararren ‘dan wasan Duniya, Ronaldo ya yi wani dogon jawabi da ya musanya jitar-jitar da ake yi na zai tashi daga Juventus, ko kuma kungiyar za ta sa shi a kasuwa.

An fara rade-radin ‘dan kwallon mai shekaru 35 zai koma kungiyar PSG ne bayan ganin yadda su ka yi waje daga gasar cin kofin Nahiyar Turai a hannun Lyon kwanaki.

Ronaldo ya yi amfani da shafinsa na Instagram, ya fadawa magoya bayan Juventus abin da ya ke hari. ‘Dan wasan ya ce yanzu ya shiryawa shekararsa ta uku a kungiyar.

KU KARANTA: Lionel Messi ya yi bore, ya ki zuwa wasa, Barcelona ta yi magana

Shekara mai zuwa a Juventus zan yi wasa – Ronaldo ya tabbatar da zamansa
Ronaldo ya kudiri samun nasara da Juve a badi
Asali: UGC

‘Dan wasan ya ce zai dage da karfinsa wajen cin kwallo, samun nasara, sadaukar da kai, da nuna kwarewa domin ganin Juventus sun zama zakaru a Italiya, Turai da Duniya.

‘Dan kwallon na kasar Portugal ya nuna ya shiryawa fuskantar kalubalen lashe kofi da shiga littafin tarihi a kakar wasan wannan shekara da za a shiga da kungiyar Turin.

A shekarar nan, Ronaldo ya zura kwallaye 31 a gasar Seria A ta kasar Italiya, wannan ya sa ya shiga sahun ‘yan kwallon da su ka fi kowa cin kwallaye a kakar wasa.

Da ya ke magana a Instagram, Cristiano Ronaldo ya ce ya na da burin ganin wannan shekarar da za a shiga ta fi ta baya nasara domin a farantawa dinbin magoya baya rai.

Idan ba ku manta ba a karshen kakar bana ne Juventus ta fatattaki kocinta Mauricio Sarri, ta maye gurbinsa da tsohon ‘dan wasan Italiya, Andrea Pirlo mai shekara 41.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel