An gudu ba a tsira ba: Masu kwalin karatun PhD na rige rigen neman aikin N20,000 a FG

An gudu ba a tsira ba: Masu kwalin karatun PhD na rige rigen neman aikin N20,000 a FG

- Masu kwalin karatun PhD hudu ne suke neman aiki a karkashin sabon shirin daukar ma’aikata na musamman guda 774,000 a jihar Ogun

- Har ila yau wasu masu kwalin karatu na digiri na biyu su 200 ma sun shiga tseren neman aiki

- Gwamnatin tarayya ce ta kaddamar da shirin a watan Yuli domin rage wa jama'a radadin korona, kuma za a dunga biyan wadanda suka yi nasarar shiga shirin N20,000 duk wata

Akalla masu kwalin karatun PhD hudu ne suke neman aiki a karkashin sabon shirin daukar ma’aikata na musamman guda 774,000 a jihar Ogun.

A watan Yuli ne Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin daukar ma’aikata na musamman karkashin jagorancin ma’aikatar kwadago da daukar ma’aikata.

Shirin na daga cikin matakan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na rage radadin annobar korona.

Jimlar ‘yan Najeriya 1,000 daga dukkanin kananan hukumomi 774 ne za su samu shiga shirin wanda kwamitocin jiha da aka kafa za su jagoranta.

An gudu ba a tsira ba: Masu kwalin karatun PhD na rige rigen neman aikin N20,000 a FG
An gudu ba a tsira ba: Masu kwalin karatun PhD na rige rigen neman aikin N20,000 a FG Hoto: The Cable
Asali: UGC

Za a dunga biyan wadanda suka samu shiga shirin N20,000 duk wata na tsawon watanni uku.

A bisa ga rahoton kididdiga na kwadago da aka saki a ranar Litinin, marasa aikin a Najeriya sun haura daga miliyan 20.93 a 2018 zuwa miliyan 21.76 a zango biyu na 2020.

Hakan na nufin ‘yan Najeriya fiye da miliyan 17 ne suka zama marasa aikin yi tun Disamba 2014, jaridar The Cable ta ruwaito.

A wata hira da jaridar Punch, Gbenga Obadara, shugaban daukar ayyukan na musamman a jihar Ogun, ya ce masu PhD hudu da digiri na biyu guda 200 na cikin masu neman aikin a jihar.

“Masu PhD hudu da masu digiri na biyu na cikin masu neman aikin. Talauci na yiwa al’umma katutu. Rashin aiki na kara hauhawa. Mutane masu kwalin PhD da digiri na biyu na rige-rigen neman aikin da za a biya 20,000.

KU KARANTA KUMA: Bahaushiya yar Gombe ta fantsama yanar gizo neman mijin aure

"Wannan shine matsalar. Ba zai iya samun kowa da kowa ba. Ba za mu ga laifin Gwamnatin tarayya ba,” in ji shi.

A cewarsa, kwamitin ya fara rabon fam tsawon makonni hudu da suka shige kuma kusan mutum 20,000 daga kananan hukumomi 20 na jihar ne suka samu fam din.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel