Wadanda su ke jinyar cutar COVID-19 a Najeriya sun koma 10, 000 - NCDC

Wadanda su ke jinyar cutar COVID-19 a Najeriya sun koma 10, 000 - NCDC

- Masu jinyar COVID-19 da-dama a Najeriya sun samu lafiya

- Mutum fiye da 40, 000 sun samu sauki, kuma an sallame su

- Wadanda cutar ta kashe ba su zarce mutum 1, 000 har yanzu

A ranar 26 ga watan Agusta, hukumar NCDC ta fitar da alkaluman da su ka tabbatar da cewa sama da mutum 40, 000 masu dauke da COVID-19 sun warke.

Hukumar da ke takaita yaduwar cututtuka a kasar ta ce an samu karin mutane 221 daga Kaduna, Legas da wasu jihohi 17 da aka gano su na dauke da COVID-19

Alkaluman da aka fitar a ranar Laraba sun nuna an samu karin mutane 60 masu COVID-19 a Filato, 33 a birnin tarayya Abuja, Kaduna ta na da karin mutane 26.

A jihar Ribas da Legas, an samu mutane 35 da gwaji ya nuna sun kamu da cutar. Hakan na zuwa ne watanni shida da samun bullar wannan annoba a Najeriya.

KU KARANTA: COVID-19: Mun shirya komawa bakin aiki - Malaman Jami’a

Wadanda su ke jinyar cutar COVID-19 a Najeriya sun koma 11, 000 - NCDC
Shugaban NCDC da Shugaba Buhari Hoto: Fadar Shugaban kasa
Asali: Facebook

Tun watan Mayu ba a samu karancin karin masu dauke da COVID-19 ba kamar jiya. Wannan ya sa wasu su ke ganin kamar an wuce lokacin intahar annobar a kasar.

Zuwa yanzu akwai mutane 40,281 da su ka warke daga cutar murar. Hakan ya na nufin an samu karin mutane 317 daga cikin adadin wadanda su ka samu lafiya a jiya.

Kamar yadda hukumar NCDC ta bayyana, mutum 1, 010 aka tabbatar sun mutu a sanadiyyar cutar nan ta COVID-19. Adadin bai kama kafar hasashen da aka yi a baya ba.

A jiya an samu labarin mutuwar mutane uku da su ke jinya, wannan ne ya sa alkaluman masu rasuwa ya tashi. Kason wadanda aka rasa har yanzu bai zarce 2% ba.

Daga lokacin da wannan cuta ta shigo zuwa yau, an yi wa mutane 380, 000 gwaji, sakamako ya nuna mutane 53, 021 su ka kamu da cutar, wanda da-damansu sun warke.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng