Abin alfaharinmu: Harshen Hausa ya zamo yare mafi saurin yaduwa a duniya
- Harshen Hausa ya kasance yare na biyu da aka fi yi kuma yana yaduwa cikin sauri
- Shugaban kungiyar Hausawa na Afrika, Dr Abdulkadir Labbaran Koguna, ya yi ikirarin cewa ana amfani da yaren Hausa a fadin duniya
- A cewarsa, majalisar dinkin duniya ta san da zaman yaren a matsayin na 11 cikin yaruka 70,250 na duniya
An bayyana harshen Hausa a matsayin daya daga cikin yaruka mafi saurin yaduwa kamar yadda ake amfani da ita a yankunan duniya da dama.
Da yake magana a kan shaharar yaren, shugaban kungiyar al’umman Hausawa na duniya, Dr Abdulkadir Labbaran Koguna, ya yi ikirarin cewa ana amfani da yaren a fadin duniya gaba daya.
Koguna ya yi wannan ikirari ne a wajen bikin ranar Hausa ta duniya na 2020 wanda aka gudanar a karamar hukumar Rano da ke jihar Kano.

Asali: UGC
A cewar Koguna, wani sashi a majalisar dinkin duniya ya san da zaman harshen Hausa sannan ya sanya ta a matsayin na 11 cikin yaruka 70,250 na duniya, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Koguna ya ce: “Baya ga wannan, masarautar Saudiyya ma ta san da zaman yaren domin yana a cikin yaruka goma da aka fassara hudubar ranar Arafat na wannan shekarar.”
Har ila yau daga cikin wadanda suka yi magana a taron harda Farfesa Abdulqadir Dangambo, wanda ya bukaci gwamnati da ta bunkasa yaren ta hanyar amfani dashi a matsayin yare na daya musamman a arewa.
A halin da ake ciki, akwai wasu abubuwan ban sha’awa game da kabilar Hausa. Kabilar ce mafi girma a nahiyar Afrika da mutane miliyan 78.
KU KARANTA KUMA: Halima Abubakar: A yanke mazakutar wanda aka kama da laifin fyade
Harshen Hausa ne yare na biyu da aka fi amfani dashi a gida tare da kimanin mutum miliyan 120 da ke yinta.
Ana iya samun masu amfani da yaren a Najeriya, Nijar, Chadi, Benin, Kamaru, Togo, Jumhuriyar Afrika ta tsakiya, Ghana, Sudan, Eritrea, Equatorial Guinea, Gabon, Senegal, da Gambia.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng