'Yan sanda sun ceto wasu yara kanana guda 2 da aka garkame a cikin bandaki a Abuja

'Yan sanda sun ceto wasu yara kanana guda 2 da aka garkame a cikin bandaki a Abuja

- An samu nasarar ceto wasu yara guda biyu da matar da take rike su ta kulle a cikin bandaki a Abuja

- Yaran masu shekaru 9 a duniya, an ruwaito cewa dama haka matar ta saba yi musu, inda take barin su da yunwa sannan ta rufe su a cikin bandaki har zuwa lokacin da za ta dawo daga wajen aiki can cikin dare

- A karshe dai jami'an 'yan sanda na yankin Garki sun samu nasarar cafke matar, inda suka wuce da ita ofishinsu don gabatar da bincike a kanta

Jami'an rundunar 'yan sanda na babban birnin tarayya Abuja sun samu nasarar ceto wasu yara guda biyu da ake zargin an rufe su a cikin bandaki a wani gida dake Garki cikin birnin na Abuja.

A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Anjuguri Manzah, ya fitar ya ce, yaran guda biyu sun fuskanci cin zarafi daga wajen mutanen da suke rike dasu wadanda ke zaune a hawa na biyu daga cikin gidajen dake FCDA Quarters, Garki.

'Yan sanda sun ceto wasu yara kanana guda 2 da aka garkame a cikin bandaki a Abuja
'Yan sanda sun ceto wasu yara kanana guda 2 da aka garkame a cikin bandaki a Abuja
Asali: UGC

Ya ce daya daga cikin yaran, Wisdom Christopher mai shekaru 9, wanda yace ya samu ya kubuta daga tagar gidan da aka kullesu, ya kira mutane inda suka samu suka ceto dayan mai suna Angel Nwoga, mai shekaru 9 a duniya shi ma.

Ya ce daya yaron 'yan sandan dake aiki a yankin Garki ne suka samu suka ceto shi da kuma wasu daga cikin jami'an hukumar kashe gobara.

A cewar shi, matar dake kula da yaran Mrs. Loveth llobi, an ruwaito cewa dama ta saba cin zarafin yaran a lokuta da dama.

"Rahotanni sun nuna cewa dama ta saba barin yaran da yunwa ta kuma kulle su a cikin bandaki har zuwa lokacin da za ta dawo daga wajen aiki can cikin dare," ya ce.

Manzah ya ce jami'an hukumar 'yan sandan sun kama matar, inda suka wuce da ita ofishinsu dake Garki domin gabatar da bincike a kanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel