Da dumi-dumi: Jigon jam'iyyar APC da mutum sama da 3,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a jihar Edo

Da dumi-dumi: Jigon jam'iyyar APC da mutum sama da 3,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a jihar Edo

- Jigo a jam'iyyar APC mai mulki, Frank Osayande, ya koma jam'iyyar PDP gabannin zaben gwamnan jihar Edo

- An ruwaito cewa Osayande ya koma jam'iyyar PDP tare da sama da mutum 3,000 na jam'iyyar APC

- Jigon jam'iyyar APC din ya ce ya yanke shawarar komawa PDP ne saboda cigaba da gwamnatin Obaseki ta kawo a jihar

A daidai lokacin da zaben gwamnan jihar Edo ke karatowa, babbar jam'iyyar APC mai mulki tayi asarar daya daga cikin jigon jam'iyyar, inda ya canja sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Jigon jam'iyyar ta APC dake Ward 9, Okokhua, cikin karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabas, Frank Osayande, ya jagoranci sama da mutum 3,000 na jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP.

Da dumi-dumi: Jigon jam'iyyar APC da mutum sama da 3,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a jihar Edo
Da dumi-dumi: Jigon jam'iyyar APC da mutum sama da 3,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a jihar Edo
Asali: Twitter

Legit ta gano cewa wadanda suka canja shekar sunyi hakane domin nuna goyon bayansu wajen sake zaben gwamnan jihar Godwin Obaseki.

Sun samu tarba ta musamman daga wajen shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Cif Dan Orbih, a lokacin yakin neman zabe da aka gabatar a jihar.

Osayande ya ce ya yanke shawarar komawa jam'iyyar ta PDP saboda cigaba da gwamnatin Obaseki ta kai jihar.

KU KARANTA: Sunaye: Jam'iyyar PDP ta ware kwamiti ta mutum 145 da zasu yi yakin neman zaben gwamnan jihar Ondo

Ya ce; "Na yanke shawarar dawowa PDP ne saboda gwamna yana yin aikin da ya kamata ga mutane, duk da dai cewa akwai mutanen da basa kaunar shi a jihar.

"Na sanar da mabiyana tun a farkon fari cewa duk inda Obaseki yayi zamu bi shi. Ba zan iya zama a jam'iyyar da bata komai ba, wato APC.

"Saboda hakane ya sanya na yanke shawarar dawowa jam'iyyar PDP tare da sama da mutum 3,000 saboda mu samu mu kawo yankin Okokhua baki daya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel