Sai da na sake kashe wata mata bayan tserewar da na yi daga hannun ‘yan sanda – Kwararren makashi Shodipe

Sai da na sake kashe wata mata bayan tserewar da na yi daga hannun ‘yan sanda – Kwararren makashi Shodipe

Sunday Shodipe, madugun mai kashe mutane a Ibadan ya bayyana cewa ya sake kashe wata mata bayan da tsere daga ofishin yan sandan Mokola inda aka tsare shi.

Shodipe ya bayyana cewa ya gudu daga ofishin yan sanda domin aiwatar da wasu tsafe-tsafe don ra’ayin wani Idris Ajani, matsafi mai shekaru 50 wanda aka kama tare da shi.

Ya fadi hakan ne a ranar Laraba, 26 ga watan Agusta, yayinda kwamishinan yan sandan jihar Oyo, Nwachukwu Enwonwu, ya gurfanar da shi.

Wanda ake zargin ya ce matsafin ya fada masa cewa da an samu matsala sosai da bai samu ya tsere don ci gaba da kashe-kashen ba, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Sai da na sake kashe wata mata bayan tserewar da na yi daga hannun ‘yan sanda – Kwararren makashi Shodipe
Sai da na sake kashe wata mata bayan tserewar da na yi daga hannun ‘yan sanda – Kwararren makashi Shodipe Hoto: The Cable
Asali: UGC

Shodipe ya ce: “Baba (matsafin) ya sha fada ma jami’in dan sanda Funsho cewa ya bude kofa domin ya barmu mu yi wanka amma jami’in bai kula mu ba.

“Daga bisani sai Baba ya fada ma jami’in cewa yana bukatar shan barasa a matsayinsa na matsafi domin hana bakaken aljanu shanye masa jini amma jami’in ya ki kula shi.

“Baba na ta ganin laifina na fadawa ‘yan sanda da jama’a ccewa shine ya tura ni kisa sannan cewa da an sallame ni idan da na ki fadin gaskiya.

“Baba ya kuma fada mani cewa wani mummunan abu na iya faruwa da shi idan ya dade tsare a hannun yan sanda saboda wasu tsafe-tsafe da bai samu ya yi ba tun bayan da aka kama shi.

“Don haka, da dan sandan ya barni na fita wanka da yamma da misalin karfe 7:00 na yamma, sai na yi amfani da wannan damar na gudu sannan na je Akinyele na kashe wata mata.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade a manyan hukumomi tara

“Baba ya tura ni waje sannan ya sani yin kisa ta hanyar ambatan sunansa, Idris Adedokun Yunusa Ajani, a cikin surkulle. Don haka sai na kashe matar domin tabbatar da tsiratar da rayuwan Baba.”

Kamar yadda kwamishinan yan sandan jihar ya tabbatar, za a mika wanda ake zargin zuwa gidan gyara halayya, wanda dama an aiye shi a ofishin yan sanda ne saboda cunkoson kurkukun jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng