Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade a manyan hukumomi tara
- Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade a ma’aikatar labarai da al’adu
- An nada shugabanni tara na hukumomi da dama a ma’aikatar, ciki harda kamfanin dillancin labaran Najeriya
- Nadin zai fara aiki daga ranar Talata, 1 ga watan Satumba, 2020
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin manyan shugabanni na hukumomi tara a karkashin ma’aikatar labarai da al’adu ta tarayya.
A wata sanarwa da aka wallafa a shafin twitter na fadar shugaban kasar Najeriya, t ace wasikar amincewa da nade-naden ya isa ga ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ta hannun Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikatan shugaban kasa a ranar Talata, 25 ga watan Agusta.
Legit.ng ta tattaro cewa nade-naden za su fara aiki daga ranar Talata, 1 ga watan Satumba, 2020.

Asali: UGC
KU KARANTA KUMA: Buhari ya koka a kan yadda shari'ar manyan laifuka ke tafiyar 'Hawainiya'
Ga jerin sabbin nade-naden a kasa:
Mista Buki Ponle – Manajan Daraktan kamfanin dillancin labaran Najeriya
Mista Nura Sani Kangiwa – Darakta Janar na cibiyar bakunci da yawon bude ido
Mista Francis Ndubuisi Nwosu – Babban sakatare, kungiyar labarai ta Najeriya
Mista Ebeten William Ivara, Darakta Janar, hukumar zane-zane ta kasa
Mista Olalekan Fadolapo – Shugaban kungiyar tallace-tallace na Najeriya
Farfesa Sunday Enessi Ododo – Janar Manaja hukumar wasan kwaikwayo na kasa
Mista Ado Mohammed Yahuza – shugaban cibiyar al’adu ta kasa
Farfesa Aba Isa Tijjani – Darakta Janar na gidan tarihi da ajiya na kasa
Misis Oluwabunmi Ayobami Amao – Darakta anar na cibiyar kayan al’adu na bakar fata da Afrika
KU KAARANTA KUMA: Buhari ya amince da yi wa attajiran 'yan Najeriya karin kudin wutar lantarki
A gefe guda, mun ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da sakatarorin dindindin guda goma sha biyu kafin a fara taron Majalisar Zartarwa ta Kasa karo na 13 da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar intanet a Abuja.
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya samu hallartar taron rantsarwar da aka yi a dakin taron majalisar da ke fadar shugaban kasa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng