Buhari ya koka a kan yadda shari'ar manyan laifuka ke tafiyar 'Hawainiya'

Buhari ya koka a kan yadda shari'ar manyan laifuka ke tafiyar 'Hawainiya'

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gabatar da jawabi a wurin taron kungiyar lauyoyi na kasa (NBA)

- Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ne ya wakilci shugaba Buhari tare da karanta jawabinsa a wurin taron.

- A cikin jawabinsa, shugaba Buhari ya koka da yadda kotunan Najeriya ke daukan lokaci kafin su zartar da hukunci a kan shari'u

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya koka da yadda kotunan Najeriya ke daukan lokaci kafin su zartar da hukunci tare da bayar da shawarar yanke hukunci a kan shari'un kanana da manyan lafuka a cikin watanni 12 da 15.

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa da ya gabatar a wurin taron kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) wanda ya halarta ta yanar gixo.

A cikin jawabin, wanda mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya karanta, Buhari ya yi waiwayen baya a kan yadda ya shafe lokuta ma su yawa a kotu a cikin shekarar 2003, 2007, da 2011 a kan zabe.

"Ban samu nasara ba adukkan lokutan uku. Amma, sai nake mamaki a wancan lokacin, me yasa za a dauki irin wannan lokaci mai tsawo kafin yanke hukunci, da kuma na samu nasara a kotun, ya za a yi kenan bayan shugaban da ke kai ya shafe shekaru a kan kujerar mulki.

Buhari ya yi korafi da bangaren shari'a
Buhari
Asali: Facebook

"A shekarar 2019 kuma ni aka kai kara kotu, na zama daya daga cikin mutanen da Atiku ke kara bayan kammala zaben shugaban kasa. Amma cikin watanni shidda kacal kotu ta yanke hukunci. Wanne banbanci aka samu kenan daga wancan lokutan zuwa yanzu?

DUBA WANNAN: Sakamakon rikicin makiyaya da manoma a Nigeria, anyi asarar akalla $12b

"An samu sauyin dokoki daga 2003, 2007 da 2011. An kawo tsarin kayyade lokacin sauraron shari'un zabe. Dole a kammala komai cikin watanni shidda zuwa takwas.

"Abin tambayar a nan shine; me yasa ba za a iya yin irin wannan tsari a kan shari'un manyan laifuka ba? me yasa kotun koli ba zata saka dokar watanni 12 domin kammala sauraro da yanke hukunci a kan shari'ar manyan laifuka ba?

"Haka ya kamata a yi wa sauran dukkan shari'un, wannan itace hanyar cigaba," a cewar wani bangare na jawabin shugaba Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel