Mahaifina na matukar son cin kosai mai sanyi da biredi da yake raye – Musa ‘Yar’adua

Mahaifina na matukar son cin kosai mai sanyi da biredi da yake raye – Musa ‘Yar’adua

- Dan marigayi tsohon shugaban kasa, Umar Musa ‘Yar’adua, ya bayyana cewa mahaifinsa na matukar son cin kosai mai sanyi da biredi da miya a lokacin da yake raye

- Musa ya bayyana mahaifinsa a matsayin mutum mai saukin kai sosai domin a cewarsa babu wanda ya biyo shi ta wannan fanni a cikinsu

- Ya ce yana matukar farin ciki game da yadda 'yan Najeriya suke yaba wa mahaifinsa saboda ayyukan da ya yi wa kasar

Musa ‘Yar’adua, dan marigayi tsohon shugaban kasa, Umar Musa ‘Yar’adua, ya bayyana cewa mahaifinsa na matukar son cin kosai mai sanyi da biredi da miya a lokacin da yake raye.

Musa ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC a ranar Talata, 25 ga watan Agusta.

Ya jaddada cewa mahifinsa mutum ne mai saukin kai sosai, domin a cewarsa duk cikinsu babu wanda ya dauko irin saukin kai na mahifin nasu.

Mahaifina na matukar son cin kosai mai sanyi da biredi da yake raye – Musa ‘Yar’adua
Mahaifina na matukar son cin kosai mai sanyi da biredi da yake raye – Musa ‘Yar’adua Hoto: The Nigerian Voice
Asali: UGC

“Mahaifina yana son kosai amma da sanyi, kuma sai can tsakar dare, sannan yana son biredi da miya. Shi mutum ne wanda tsakani da Allah yana da saukin kai. Ko a cikin gidanmu gaskiya ba wanda ya biyo wannan hali ta wannan fannin...zai dawo daga aiki ya ci kosai hankalinsa ya kwanta,” in ji shi.

Ya kara da cewa yana matukar farin ciki game da yadda 'yan Najeriya suke yaba wa mahaifinsa saboda ayyukan da ya yi wa kasar, yana mai cewa "hakan na nufin duk abin da mutum zai yi ya kamata ya zama mutumin kirki."

KU KARANTA KUMA: Bayan shekaru 13: Gwamna Zulum zai gudanar da zaben kananan hukumomin Borno

Musa 'Yar'adua ya ce yana alfahari da kasancewa daga zuriyar da ta yi wa Najeriya hidima musamman ganin cewa kakansa, Musa Yar Adua, ya taba zama minista a gwamnatin farar hula ta farko.

Sannan kawunsa Shehu Yar Adua ya zama mataimakin shugaban kasa kuma mahaifinsa ya zama shugaban kasa.

Ya ce babban burinsa shi ne ya tabbatar bai bata sunan zuriyarsu ba musamman kan rawar da suka taka wajen cigaban Najeriya.

Sai dai Musa ‘Yar’Adua ya kara da cewa ba shi da niyyar shiga harkokin siyasa, sai dai ya tabbatar da cewar a shirye yake ya bayar da tasa gudummawar wajen cigaban Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel