A raba ni da matata Amina domin ta yi kokarin sanya mani guba – Magidanci ya sanar da kotu

A raba ni da matata Amina domin ta yi kokarin sanya mani guba – Magidanci ya sanar da kotu

- Kotu ta rushe auren shekaru 14 tsakanin wani mai suna Dauda Saliman da matarsa Amina, kan zarginta da yunkurin ba mijinta guba

- Alkalin kotun, Cif Ademola Odunade da wasu masu sasanci biyu sun ce an rushe auren ne domin wanzar da zaman lafiya a tsakani

- An kuma mika ragamar kula da yaran a hannun mahaifiyarsu, inda mahaifinsu zai ci gaba da daukar dawainiyarsu

Wata kotun gargajiya da ke zama a Mapo, Ibadan a ranar Talata, 25 ga watan Agusta, ta rushe auren shekaru 14 tsakanin wani mai suna Dauda Saliman da matarsa Amina, kan zarginta da yunkurin ba mijinta guba.

Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade da wasu masu sasanci biyu sun ce an rushe auren ne domin wanzar da zaman lafiya a tsakani.

Ya mika ragamar kula da yara uku da suka aifa a auren ga wacce ake kara wato mahaifiyarsu kenan, jaridar The Nation ta ruwaito.

A raba ni da matata Amina domin ta yi kokarin sanya mani guba – Magidanci ya sanar da kotu
A raba ni da matata Amina domin ta yi kokarin sanya mani guba – Magidanci ya sanar da kotu Hoto: Thisday
Asali: Twitter

Har ila yau ya umurci wanda ke karan wato mijin kenan da ya dunga biyan N15,000 a matsayin kudin abincin yaransa duk wata sannan kuma shine zai dunga daukar dawainiyar karatunsu da sauran harkokinsu.

KU KARANTA KUMA: Saboda haihuwar tagwaye: Magidanci ya tsere ya bar matarsa da 'ya'yansa

Odunade ya nuna bacin rai a kan halayyar Amina na barin mijinta ya koma otel da kwana tsawon shekaru uku ba tare da ta koka a kan hakan ba.

Ya bayyana cewa ita ce umul-aba’isin abunda duk ya same ta.

A wani labarin, wani malamin addini, Adebayo Bamidele, ya roki kotun gargajiya da ke zama a Mapo, Ibadan, da ta rushe aurensa na shekaru 17 da matarsa Felicia, kan hujjar cewa tana lalata masa harkoki.

Bamidele ya fada ma kotun a ranar Talata cewa matarsa na aikata abubuwan da ke lalata masa kiran da yake zuwa ga Ubangiji.

“Tana yi mun zarge-zarge masu lalata suna a gaban mabiyana.

“Ta mayar da ni mara aikin yi.

“Duk mabiya na sun bar coci na,” in ji shi.

Faston ya ci gaba da fada ma kotun cewa wasu mambobin cocin sun nakada masa dukan tsiya biyo bayan zarge-zargen da Felicia ta yi a kansa.

“Felicia ta fada masu cewa ina amfani da bakaken aljanu da sihiri wajen kwashe masu arzikinsu.

“Sun yi mun mugun duka, sun yaga mun kayana.

“Har na kusa mutuwa.

“A yanzu tana ikirarin cewa cocin nata ne.

“Maganar gaskiya shine mun hada kudi wajen gina cocin, na rasa hanyar samuna saboda mugun nufinta a kaina,” in ji shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel