Ambaliyar ruwa: Rayuka 5, dubban gidaje da gonaki sun salwanta a Sokoto
Mutane biyar suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta debe dubban gidaje da gonaki a karamar hukumar Goronyo da ke jihar Sokoto.
Daily Trust ta gano cewa, ambaliyar ruwan ta hada da dabbobin da ake kiwo tare da hatsi.
A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, shugaban yankin, Zakari Muhammad Shinaka ya ce sama da gidaje 2000 ne suka salwanta a garin Rimawa kadai.
Ya kara da cewa, gidaje masu tarin yawa da gonaki sun salwanta a Katsira, Kagara, Gorau, Birjingo, Shinaka da wani bangare na Sabon Garin Dole.
Sauran wuraren da ambaliyar ruwan ta shafa ya hada da Rimawa, Tulaske, Kwakwaza, Ilela Huda da Danwaru tare da sauran wuraren da ke da kusanci da ruwa.
Daga cikin amfanin gonar da ambaliyar ruwan ya tafi da su sun hada da shinkafa, dawa, gero da masara.
Ya yi bayanin cewa, wani tsoho da 'ya'yansa biyu sun rasa rayukansu sakamakon faduwar gini a Gebe. Wasu karin mutum biyu sun rasu sakamakon ibtila'in a kauyen Giyawa.
KU KARANTA: Kano: Mata mai tsohon ciki ta rasu bayan mijinta ya garkameta na kwanaki
Ya tabbatar da cewa, tuni Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya umarcesu da su dauka yawan rashe-rashen da aka yi da asarorin.
Gwamnan ya umarci hukumar taimakon gaggawa da su tabbatar da cewa an gaggauta kai wa wadanda abun ya shafa kayan rage radadi tare da tallafi daga NEMA.
A daya bangaren, Shinaka ya ce shugabannin karamar hukumar sun samarwa da wadanda abun ya shafa buhuna inda suka hada gidaje na wucin-gadi.
A wani labari na daban, yadda makamai ke samuwa a jihar Zamfara ya samo asali ne daga yadda bakin hauren ke musayar makamai da zinaren da ake hakowa a jihar, Gwamna Bello Matawalle ya sanar da hakan a ranar Talata.
Kamar yadda yace, wannan lamarin yasa bakin hauren ke musaya da zinaren da ake hakowa ba da sanin gwamnati ba, kuma hakan ya bada gudumawa wurin yaduwar makamai a jihar.
Ayyukan 'yan bindiga a koda yaushe kara kamari yake yi a jihar Zamfara da sauran jihohin da ke yankin arewa maso yamma na kasar nan.
Gwamnan ya sanar da hakan ne bayan ganawar da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidan gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin.
Matawalle ya ce ya ziyarci shugaban kasar ne don neman shawara da taimakon yadda za a magance rashin tsaro da kuma hakar zinare da ake yi a jihar ba bisa ka'ida ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng