Gwamnan Zamfara: Bakin haure ke karbar zinari suna bai wa 'yan bindiga makamai

Gwamnan Zamfara: Bakin haure ke karbar zinari suna bai wa 'yan bindiga makamai

Yadda makamai ke samuwa a jihar Zamfara ya samo asali ne daga yadda bakin hauren ke musayar makamai da zinaren da ake hakowa a jihar, Gwamna Bello Matawalle ya sanar da hakan a ranar Talata.

Kamar yadda yace, wannan lamarin yasa bakin hauren ke musaya da zinaren da ake hakowa ba da sanin gwamnati ba, kuma hakan ya bada gudumawa wurin yaduwar makamai a jihar.

Ayyukan 'yan bindiga a koda yaushe kara kamari yake yi a jihar Zamfara da sauran jihohin da ke yankin arewa maso yamma na kasar nan.

Gwamnan ya sanar da hakan ne bayan ganawar da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidan gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin.

Matawalle ya ce ya ziyarci shugaban kasar ne don neman shawara da taimakon yadda za a magance rashin tsaro da kuma hakar zinare da ake yi a jihar ba bisa ka'ida ba.

Gwamnan ya ce "bakin haure ke shiga jihar farautar zinaren da sauran albarkatun da suke da su. A maimakon siya da kudi, suna biya ne da makamai. Na yi wasu bincike."

Gwamnan Zamfara: Bakin haure ke karbar zinarin suna bai wa 'yan bindiga makamai
Gwamnan Zamfara: Bakin haure ke karbar zinarin suna bai wa 'yan bindiga makamai. Hoto daga Gwamna Bello Matawalle
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga muhimmiyar ganawa da Buni da Ganduje

Kamar yadda Legit.ng ta wallafa, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle a ranar Litinin 24 ga watan Agusta ya kai wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Matawalle ya gabatarwa da shugaban kasar gwala-gwalan da wasu ma’adinai daban-daban da aka hako a jihar Zamfara.

Alhaji Bashir Hadejia ne ya yi wa Gwamna Matawalle rakiya yayin ziyarar da ya kai fadar shugaban kasar a daren jiya Litinin domin gabatar wa shugaba Buhari ma'adinan.

Hadimin shugaban kasa a kan kafafen watsa labarai, Buhari Sallau yana daga cikin wadanda suka wallafa hotunan ziyarar a dandalin sada zumunta.

Ya rubuta cewa, "Shugaba Muhammadu Buhari a daren jiya a gidansa, wato gidan gwamnati da ke Abuja ya karbi bakuncin Gwamnan jihar Zamfara, Dakta Bello Muhammad Matawalle da Alhaji Bashir Hadejia ya yi wa rakiya.

"Gwamna Matawalle ya ziyarci gidan gwamnatin ne domin ya gabatar da gwala-gwalai da wasu maadinai masu daraja da aka hako a jiharsa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel