Hotuna: Kamfanin mota na Najeriya ya gwangwaje hukumar 'yan sanda da motoci masu dan karen kyau

Hotuna: Kamfanin mota na Najeriya ya gwangwaje hukumar 'yan sanda da motoci masu dan karen kyau

- An bawa hukumar 'yan sandan Najeriya motoci masu kyau

- Hukumar 'yan sandan ta samu kyautar motocin ne guda uku daga wurin kamfanin motoci na Najeriya na Innoson domin taimakawa wajen gabatar da ayyuka a fadin kasa

A kokarin da take na taimakawa al'umma, kamfanin motoci na Innoson dake Najeriya ya bayar da kyautar motoci guda uku ga hukumar 'yan sandan Najeriya.

A sanarwar da kakakin hukumar 'yan sandan na kasa, Frank Mba, ya fitar, shugaban hukumar 'yan sanda na kasa ya karbi wadannan motoci guda uku daga wajen wannan kamfanin.

Motocin masu kirar Innoson G12 Series, an mika su ga hukumar 'yan sandan Najeriyan ta hannun Jonas Maduabuchukwu Ojukwu a madadin shugaban kamfanin Cif Innocent I. Chukwuma.

Hotuna: Kamfanin mota na Najeriya ya gwangwaje hukumar 'yan sanda da motoci masu dan karen kyau
Hotuna: Kamfanin mota na Najeriya ya gwangwaje hukumar 'yan sanda da motoci masu dan karen kyau
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zamu sake tsunduma ma'aikata 774,000 da zamu dauka cikin harkar noma bayan kammala aikinsu na wata uku - Gwamnatin tarayya

Shugaban hukumar 'yan sandan da ya samu wakilcin DIG Abdulmajid Ali, ya bayyana cewa "bayar da taimako a wannan yanayi, babu shakka hukumar 'yan sandan Najeriya za ta samu nasarar kawo karshen ta'addanci a kasar nan."

Ali ya bukaci sauran al'umma da kamfanoni da suyi koyi da wannan halayya mai kyau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel