Najeriya: Tattalin arziki ya karye da – 6%, abin da aka dade ba a gani ba

Najeriya: Tattalin arziki ya karye da – 6%, abin da aka dade ba a gani ba

Tattalin arzikin kasar Najeriya ya durkushe a cikin shekarar nan ta 2020. Alkaluman da aka fitar na rubu’in bana sun nuna tattalin kasar bai iya motsawa gaba ba.

Asali ma tattalin kasar ya durkushe ne da maki – 6.10%, hakan ya na nufin tattalin arzikin Najeriya ya motsa baya ne maimakon ya yi gaba a tsakiyar wannan shekara.

Jaridar Daily Trust ta ce wannan ne mafi munin halin da aka shiga tun shekarar 2010. Tsakanin 2016 da 2017 tattalin kasar ya karye, amma munin bai kai irin haka ba.

Bloomberg ta yi hasashen tattalin arzikin kasar nan zai karye da 4%, a karshe alkaluman NBS sun nuna cewa tasirin COVID-19 ya jawo tattalin ya durkushe da kashi 6%.

Hakan ya na zuwa ne jim kadan bayan an samu rahoton cewa mutane fiye da miliyan 21 ba su da aikin yi a Najeriya. Wannan zai iya haddasa yawan aukuwar laifuffuka.

Babban abin da ya jawowa Najeriya wannan durkushewar tattali ita ce annobar COVID-19, wanda ta nakasa kasashen Duniya da-dama, daga ciki har da Amurka da Ingila.

KU KARANTA: ‘Dan Majalisa zai kai Gwamnati kotu a kan shirin bada aiki

Najeriya: Tattalin arziki ya karye da – 6%, abin da aka dade ba a gani ba
Ministar Tattalin arziki, Zainab Ahmed
Asali: UGC

A cikin bara, an yi dace tattalin kasa ya motsa da 2.12%, hakan ya na nufin idan aka kamanta lokutan biyu, za a ga an ci baya da akalla -8.2% a tsakiyar wannan shekara.

Hukumar NBS ta ce bangaren masana’antu da ma’adanai ya karye da – 6.05% a farkon bana, akasin zaburar 1.64% da aka samu a makamancin wannnan lokaci a cikin bara.

A yanzu, mai ne ya bada fiye da kaso 90% na jimillar tattalin arzikin Najeriya na GDP. Sauran bangarori sun samar da 8.93% kacal a lokacin da ake kokarin fadada tattalin kasar.

Duk da halin da aka shiga, bangaren ICT ya bada gudumuwar 17.8% a bana. Wannan kaso ya zarce abin da aka samu a shekarar da ta gabata kamar yadda rahotanni su ka nuna.

‘Yan Najeriya da-dama su na kukan tashin farashin kayan abinci a kasuwanni, haka zalika kudin man fetur ya na kara tsada, yayin da kudin da mutane su ke samu bai wani karu ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel