ISWAP: Sojin sama sun ragargaza kwamandojin 15 a jihar Borno

ISWAP: Sojin sama sun ragargaza kwamandojin 15 a jihar Borno

Dakarun sojin sama na Operation Lafiya Dole, sun samu manyan nasarori a kan mayakan ta'addanci na ISWAP da ke aika-aika a yankin tsibirin tafkin Chadi da ke Arewacin jihar Borno.

Wannan ya faru ne a ranar 24 ga watan Augustan 2020 a wani gagarumin hari da dakarun suka kai musu a karkashin Operation Hail Storm a Kira Wulgo da Sabon Tumbun.

Yankuna biyu ne na tafkin Chadi inda aka halaka manyan shugabannin ISWAP da mayakan ta'addancin.

Dakarun sun kai samamen ne bayan gamsassun rahotanni da suka samu da ke bayyana cewa shugabannin ISWAP da mayakansu sun koma Sabon Tumbun, saboda ragargaza su da aka yi a yayin da suke tsibirin kusa da Tumbuna Baba.

Hakazalika, manyan kwamandojin ISWAP a kalla 15 aka halaka a Kira Wulgo, inda suka mayar babbar hedkwatarsu kuma wurin horarwar mayakan ta'addancin.

ISWAP: Sojin sama sun ragargaza kwamandojin 15 a jihar Borno
ISWAP: Sojin sama sun ragargaza kwamandojin 15 a jihar Borno. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda hadimin Ganduje ya assasa rikici a Kano, an soka wa dattijo wuka

Dakarun sojin saman sun aika da jiragen yaki da na bindigogi wadanda suka kai hari wuraren biyu, lamarin da ya kawo gagarumar nasarar.

Fitattun shugabannin ISWAP da aka kashe a wannan samamen sun hada da Abu Imraana, kwamandan ISWAP na ruwa tare da Mallam Ibrahim da Mallam Abba, wanda aka gano suna cikin mamatan.

Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na zakakuran sojin, Manjo janar John Enenche, ya bayyana, shugaban sojin saman Najeriya, ya jinjinawa sojin inda ya yi kira garesu da su ci gaba da tabbatar da kawo karshen ta'addanci a yankin arewa maso gabas na kasar nan.

A wani labari na daban, dakarun Sojin Najeriya karkashin atisayen Operation Sahel Sanity, sun damke yan bindiga akalla 150 kuma sun hallaka daya a jihar Zamfara.

Mukaddashin diraktan harkokin yada labarai rundunar, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan a Faskari, jihar Katsina ranar Talata.

Onyeuko ya ce Sojin sun gano wata mabuyar yan bindigan dake Gadan Zaima inda sukayi ram da su. Ya kara da cewa yan bindigan da aka damke suna hannun yan sanda kuma an kaddamar da bincike kansu.

Ya ce za'a mikasu hannun yan sanda na ba da dadewa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel