Musulman Lauyoyi sun bukaci a hana Wike, Obasanjo da Blair magana a taron NBA

Musulman Lauyoyi sun bukaci a hana Wike, Obasanjo da Blair magana a taron NBA

Kungiyar MULAN ta musulman lauyoyi na kasa, ta zargi takwararta NBA da rashin adalci da nuna banbamci a soke gayyatar da ta yi wa gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

NBA ta cire Nasir El-Rufai daga cikin wadanda za su yi magana a taronta na wannan shekara. Kungiyar ta ce ta yi wannan ne saboda saba dokar kasa da ake kukan gwamnan ya na yi.

MULAN ta bukaci kungiyar NBA ta soke bangaren jawabin Nasir El-Rufai a taron, ko kuma ta cire sunan duk wani da aka taba samu da irin laifin da ake zargin gwamnan da aikatawa.

Jaridar Premium Times ta ce hakan na zuwa ne bayan wasu rassan kungiyar NBA sun fito su na cewa ba za su halarci taron wannan shekara ba, muddin ba a dawo da sunan gwamnan ba.

Kungiyar MULAN ta fitar da jawabi ne ta bakin shugabanta, Farfesa Abdulqadir Abikan da sakatarensa na kasa, Ibrahim Alasa. MULAN ta soki yadda NBA ta dauki wannan mataki.

A jawabin da MULAN ta fitar, ta ce ya zama dole ta tsoma baki a abin da ya ke faruwa saboda irin rashin adalcin da aka yi, da kuma murde ka’idoji da aka yi wajen gayyatar wasu dabam.

KU KARANTA: Ana zaman dar-dar, masu garkuwa da mutane sun addabi Kaduna

Musulman Lauyoyi sun bukaci a hana Wike, Obasanjo da Blair magana a taron NBA
Gungun Lauyoyi a Najeriya
Asali: UGC

A cewar kungiyar musulman, bai kamata a bada dama ga wasu da ake zargi da laifin sabawa dokar kasa ko a Najeriya ko kasashen ketare, su halarci wannan taro da za a gudanar ba.

Kungiyar ta MULAN ta ce ta fahimci cewa wasu sun yi amfani da wannan dama da uwar kungiyar NBA ta bada wajen yakar gwamna Nasir El-Rufai saboda wani sabani da ke tsakaninsu.

Bayan haka, kungiyar ta yi tir da yadda lamarin ya jawo surutu, sannan ta ce akwai mutanen da aka gayyata su yi jawabi duk da cewa ana zargin barnar da su ka tafka a baya ta na da yawa.

A dalilin wannan ne musulman su ka nemi a cire sunan tsohon firayim ministan Birtaniya, Tony Blair daga jerin masu magana a taron, saboda laifin da aka samu ya aikata a kasar Iraki.

Ana zargin Tony Blair da kai wa Iraki hari a lokacin Saddam Husseini. Duniya ta yarda wannan hari ya yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin Bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba.

Sauran wadanda ake neman NBA ta haramtawa magana a taron lauyoyin su ne tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo da gwamna Nyesom Wike, bisa zargin su na da kashi a jikinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel