Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga muhimmiyar ganawa da Buni da Ganduje

Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga muhimmiyar ganawa da Buni da Ganduje

- Jam'iyyar APC na tsananta shirye-shirye yayin da zaben jihar Edo yake karatowa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya shiga ganawa da Gwamna Mai Mala Buni a Abuja

- Taron da suka shiga ya samu halartar Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

A halin yanzu, shugaban kasa Muhammdu Buhari ya shiga ganawa ta musamman da Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano.

Ana yin taron mai muhimmanci ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata, 25 ga watan Augustan 2020 a kan zaben gwamnoni na jihar Edo da ke karatowa.

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanar da hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganawa da Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, da Gwamna Abdullahi ganduje na jihar Kano a kan zaben Edo mai karatowa," Ahmad ya wallafa a shafins ana Twitter a ranar Talata.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ce ta saka ranar 19 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ayi zaben gwamnoni na jihar Edo.

Gwamna Ganduje, wanda shine shugaban yakin neman zaben gwamnan jihar Edo, amma karkashin jam'iyyar APC, ya tabbatar da cewa sai jam'iyyar mai mulki ta kawo jihar Edo a zaben mai zuwa.

Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga muhimmiyar ganawa da Buni da Ganduje
Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga muhimmiyar ganawa da Buni da Ganduje. Hoto daga Bashir Ahmad
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda hadimin Ganduje ya assasa rikici a Kano, an soka wa dattijo wuka

Taron ranar Talatan da shugaban kasan ana sa ran shine taro na karshe da zai yi da mashirya yakin neman zaben don kwace jihar daga hannun Gwamna Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP.

A wani labari na daban, a cikin kokarin kwamitin sasanci na rikon kwarya na jam'iyyar APC wanda ya samu jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, a ranar Litinin an yi nasarar sasanta ministan sufuri, Rotimi Amaechi da takwaransa, karamin ministan man fetur, Timipre Sylva.

Dukkan ministocin sun amince za su yi aiki tare don kawo gyara a jam'iyyar a yankin kudu-kudun kasar nan.

Amaechi ya taba yin gwamnan jihar Ribas, hakazalika Sylva ya taba zama gwamnan jihar Bayelsa.

A yayin bayanin wannan ci gaban ga manema labarai, bayan tattaunawar sirri da aka yi tsakanin tsoffin gwamnonin da shugaban kwamitin rikon kwaryar a babban ofishin jam'iyyar APC a Abuja, sun tabbatar da sasancin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel