Ganduje ya dauka alarammomi 60 aiki don koyar da almajiran Kano
- Gwamnatin jihar Kano ta amince da daukar malaman Qur’ani wato Alarammomi 60 a fadin makarantun Almajiranci 15 da ke jihar
- Kwamishinan ilimi na jihar, Sanusi Kiru ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi a ranar Talata, 25 ga watan Agusta
- Za a tura malaman guda 60 zuwa sabbin makaratun kwana na Almajiranci da aka samar a kananan hukumomin Bunkure, Madobi da Bagwai
- Ya jaddada cewa Gamna Ganduje ya jajirce wajen kawar da bara a titi da kuma rashin ka’ida wajen kafa makarantun Qur’ani ba tare da samar da gine-gine da suka kamata ba
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya amince da daukar malaman Qur’ani (Alarammomi) 60 a fadin makarantun Almajiranci 15 da ke jihar.
Kwamishinan ilimi na jihar, Sanusi Kiru, a wani jawabi a ranar Talata, ya ce daukar malaman guda 60 a makarantun Almajiranci zai fara aiki ne nan take.
Ya bayyana cewa, “Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya amince da hakan biyo bayan wata wasika da hukumar makarantun Islamiyya ta jihar (KSQISMB) ta gabatar a ranar Litinin.
“Daukar wannan aiki ya sake nuna jajircewar gwamnan wajen kawar da bara a titi da kuma rashin ka’ida wajen kafa makarantun Qur’ani ba tare da samar da muhimman gine-gine da suka kamata ba.
“Wadannan gine-gine sun hada da bandaki, dakunan barci da kuma manhajar da zai sa yaran Almajirai haddace Qur’ani da sauran darusa da ake bukata cikin mutunci da tsaro,” in ji shi.
KU KARANTA KUMA: Kashe-kashen Kudancin Kaduna: Cikakken bayani kan ganawar El-Rufai da Sultan ya bayyana
Mista Kiru ya bayyana cewa za a tura malaman guda 60 zuwa sabbin makaratun kwana na Almajiranci da aka samar a kananan hukumomin Bunkure, Madobi da Bagwai.
A cewarsa, sabbin makarantun kari ne ga guda 12 da ake da su a fadin jihar, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
A wani labari na daban, cibiyar kula da bayanai da ci gaba (CITAD), ta ce ta matukar damuwa da miyagun kalaman da mai bai wa Ganduje shawara na musamman, Murtala Hamza Buhari Bakwana yayi wanda ya tada tarzoma.
An ga mai bai wa gwamnan shawara a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani inda yake zargin abokan hamayyarsu na siyasa tare da umartar 'yan daba da su kai musu hari.
Bakwana ya yi maganar ne a taron sasanci na jam'iyyar APC a kan wata rashin jituwa tsakaninshi da wasu 'yan jam'iyyar na yankin, jaridar HumAngle ta wallafa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng