Yadda hadimin Ganduje ya assasa rikici a Kano, an soka wa dattijo wuka

Yadda hadimin Ganduje ya assasa rikici a Kano, an soka wa dattijo wuka

Cibiyar kula da bayanai da ci gaba (CITAD), ta ce ta matukar damuwa da miyagun kalaman da mai bai wa Gwamna Abddullahi Umar Ganduje na jihar Kano shawara na musamman, Murtala Hamza Buhari Bakwana yayi wanda ya tada tarzoma.

An ga mai bai wa gwamnan shawara a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani inda yake zargin abokan hamayyarsu na siyasa tare da umartar 'yan daba da su kai musu hari.

Bakwana ya yi maganar ne a taron sasanci na jam'iyyar APC a kan wata rashin jituwa tsakaninshi da wasu 'yan jam'iyyar na yankin, jaridar HumAngle ta wallafa.

Kalamansa sun tada tarzoma tsakanin 'yan jam'iyyar, inda 'yan daba suka soka wa daya daga cikin dattawan jam'iyyar wuka.

Kungiyar, wacce take kula tare da kiyaye kalamai masu hatsari da kiyayya a Najeriya, ta kwatanta kalaman mai bada shawarar da na tada tarzoma.

Yadda hadimin Ganduje ya assasa rikici a Kano, an soka wa dattijo wuka
Yadda hadimin Ganduje ya assasa rikici a Kano, an soka wa dattijo wuka. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Saboda carar zakaransa da sassafe: Kotu ta ci wani tsoho tarar N77,304

"CITAD na kira da a dauka mataki a kan wannan kalaman masu iya tada tarzoma da kawo rikici.

"Mun yi matukar kushesu domin za su iya zama babbar barazana ga zaman lafiya tare da assasa rikici," kungiyar tace.

Kungiyar ta yi kira ga Ganduje da ya dauka matakin da ya dace a kan hadimin sakamakon rikicin da ya assasa. Sun jaddada cewa wadannan kalaman za su iya bude kofar barkewar rikicin 'yan siyasa a jihar Kano.

"Muna son yin amfani da wannan damar wurin jinjinawa rundunar 'yan sandan yanki ta daya na jihar kano a kan yadda suka shawo kan lamarin.

"Babu shakka hakan ya bada babbar gudumawa ga dakile tarzomar da ta fara tashi a yankin sakamakon taron siyasar," CITAD tace.

“Dole ne a ci gaba da daukar matakai irin wannan ba tare da tsoro ba ko kuma duba bangaranci.

“'Yan siyasa masu rike da mukamai bai kamata su dinga kalamai masu iya wargaza al'umma ba. A don haka dole ne a dinga kiyaye kalaman da za a fitar daga baki komai banbancin siyasa," kungiyar tace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel