Yarbawan Jam’iyyar APC sun yabawa kiran da Tanko Yakassai ya ke yi

Yarbawan Jam’iyyar APC sun yabawa kiran da Tanko Yakassai ya ke yi

Jam’iyyar APC ta reshen Kudu maso yammacin Najeriya ta jinjinawa, Tanko Yakassai na kiran da ya yi na cewa a tsaida ‘dan takarar 2023 daga Kudu.

Alhaji Tanko Yakassai ya na cikin masu ra’ayin cewa ya kamata ‘dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023 ya fito daga bangaren Kudancin kasar.

Wannan magana da Dattijon Arewan ya yi ta jawo masa yabo daga wani daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki a yankin Kudu maso yammacin Najeriya.

Sakataren yada labaran APC na yankin, Karounwi Oladapo, ya ce Yakasai wanda ya na cikin manyan dattawan Arewa ya yi amfani da tunani na hankali a wannan kira.

Cif Karounwi Oladapo ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fitar a madadin jam’iyyar APC kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana a ranar Litinin, 25 ga watan Agusta.

KU KARANTA: An yi wa Tinubu ritaya daga siyasa a APC - Fani-Kayode

Yarbawan Jam’iyyar APC sun yabawa kiran da Tanko Yakassai ya ke yi
Yakassai ya na ganin lokaci ya yi da Kudu za ta yi mulki
Asali: Twitter

Karounwi Oladapo ya nuna cikakken goyon baya ga Tanko Yakassai, duk da cewa tsohon ‘dan siyasar bai bayyana wace shiyya ce ta fi dacewa da mulkin a Kudancin kasar ba.

A ra’ayin Alhaji Yakassai, wanda ya ke siyasa tun a jamhuriyya ta farko, tun da Arewa ta samu mulki, a 2023 ya kamata a bar wa mutanen Kudu dama su dana shugabanci.

Cif Oladapo ya nuna jam’iyyar APC ta goyi bayan Yakassai kamar dai yadda ta yabawa wadanda su ka yi irin wannan kira a baya; Nasir El-Rufa, Ali Ndume, da Abdulaziz Yari.

Tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari, gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da Sanata Mohammed Ali Ndume su na cikin masu irin wannan ra’ayi na Tanko Yakassai.

Yayin da ake batun mulki ya koma Kudu, wasu su na ganin mutanen Ibo ne ya dace su yi shugabanci wannan karo, a ra'ayin wasu kuma, Yarbawa ne su ka fi cancanta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel