Buhari ya yi sabbin nade-nade shida, ya ambaci Kangiwa a matsayin shugaban PWDC

Buhari ya yi sabbin nade-nade shida, ya ambaci Kangiwa a matsayin shugaban PWDC

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabbin nade-nade guda shida

- A ranar Litinin, 24 ga watan Agusta, an ambaci sunan Hussaini Suleiman Kangiwa a matsayin shugaban hukumar nakasassu

- Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce hukuncin Buhari ya yi daidai da dokar haramta cin zarafin mutane masu nakasa na 2019

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin shugaban kungiya da babban sakataren hukumar nakasassu na kasa (PWD).

Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasar ya ambaci sunan Hussaini Suleiman Kangiwa (arewa maso yamma) a matsayin shugaba sannan James David Lalu (arewa ta tsakiya) a matsayin babban sakataren hukumar.

A wani jawabi daga mai ba shugaban kasar shawara na musamman a kafofin watsa labarai, Femi Adesina, a Abuja a ranar Litinin, 24 ga watan Agusta, ya ce matakin Buhari ya yi daidai da dokar haramta cin zarafin nakasassu na 2019.

Buhari ya yi sabbin nade-nade shida, ya ambaci Kangiwa a matsayin shugaban PWDC
Buhari ya yi sabbin nade-nade shida, ya ambaci Kangiwa a matsayin shugaban PWDC Hoto: The Cable
Asali: UGC

A cewar dokar, hukumar za ta samu jagorancin shugaba da mambobi shida wadanda za su zamo mutane masu nakasa.

Za kuma su wakilci yankunan kasar bayan majalisar dattawa ta tabbatar da su na tsawon shekaru hudu a zangon farko, sannan ana iya sake nada su a karo na biyu.

Jawabin ya sanar da cewar babban sakataren, zai kasance da alhakin aiwatar da manufofi da harkokin hukumar na yau da kullun, kuma ya kasance mai nakasa.

Sakataren zai shafe shekaru biyar a zangon farko, sannan ana iya sake nada shi a karo na biyu.

KU KARANTA KUMA: Karin 'yan Najeriya 321 sun kamu da korona, jimilla 52,548

Mambobin hukumar sun hada da Oparaku Onyejelam Jaja (kudu maso gabas), Philomena Isioma Konwea (kudu maso kudu), Omopariola Busuyi Oluwasola (kudu maso gabas).

Sauran sune Amina Rahma Audu (arewa maso yamma), Esther Andrew Awu (arewa ta tsakiya) da kuma Abba Audu Ibrahim (arewa maso gabas).

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya, a karkashin tsarin fansho na karo-karo, ta saki biliyan N14.92 domin biyan basukan hakkokin ma'aikatan da suka yi ritaya.

Hukumar kula da harkokin fansho ta kasa ce ta sanar da hakan ranar Litinin a cikin wata takarda da ta fitar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel