Gwamnatin Jihohi su na damun asusun tarin Tarayya – RMAFC

Gwamnatin Jihohi su na damun asusun tarin Tarayya – RMAFC

Hukumar RMAFC mai kula da kason albashi da kudin ma’aikata a Najeriya, ta ce ana damun asusun rabon dukiyar kasa watau FAAC.

RMAFC ta yi gargadi cewa bukatun da su ke zuwa daga bangarorin gwamnatin tarayya, jihohi da na kananan hukumomi su na yi wa asusun FAAC yawa.

Shugaban hukumar RMAFC na kasa, Injiniya Elias Mbam, ya yi kira ga gwamnatocin jihohin kasar da su fito da hanyoyin bunkasa samun kudin shigarsu.

Elias Mbam ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi alkaluman jihohi na ASVI daga hannun Editan gidan jaridar Economic Confidential, Yushau A. Shuaib.

Da ya ke magana da Yushau Shuaib a garin Abuja, Elias Mbam ya ce bukatun jihohi ya yi wa asusun kasar nauyi a dalilin dogara da jihohin su ke yi da FAAC.

“Dogaro ka-co-kam da aka yi da kason wata-wata daga FAAC ya sa ya zama dole jihohi su bunkasa hanyar samun kudin shigarsu na IGR.” Inji injiniya Mbam.

KU KARANTA: Miyagun ‘Yan bindiga sun hallaka mutane 1, 126 a Arewa - Amnesty Int’l

Gwamnatin Jihohi su na damun asusun tarin Tarayya – RMAFC
Wasu Gwamnonin Jihohi a fadar Shugaban kasa
Asali: Facebook

Ya ce: “Rahoton ASVI na shekara-shekara ya na bada bayanai, tare da taimakawa RMAFC wajen aikinta na kira ga jihohi su inganta kudin da su ke tatsa da kansu.”

Mbam ya yaba da kokarin da jaridar Economic Confidential ta ke yi, musamman wajen fitar da bayanai da alkaluma masu muhimmanci da za su taimakawa harajin jihohi.

Yushau Shuaib ya ce binciken da su ka yi ya nuna masu cewa jihohi da-dama ba za su iya gudanar da harkokin mulki ba tare da kason FAAC da su ke samu duk wata ba.

Shuaib ya ce alkaluma sun tabbatar masu da cewa akwai jihohi bakwai da abin da su ke samu daga haraji na IGR bai kai kashi 10% na kudin da su ke karba daga kason tarayya ba.

“Jihohin Ribas, Kaduna, Enugu, Kwara da Zamfara ne kawai su ke yi hobbasa wajen samun kudin shiga a 2019, idan aka kamanta da abin da su ka samu a shekarar 2018.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel