COVID-19: Bishof Stephen Mamza ya na dauke da kwayar Coronavirus

COVID-19: Bishof Stephen Mamza ya na dauke da kwayar Coronavirus

- Shugaban CAN na reshen Adamawa ya kamu da cutar Coronavirus

- Limamin Kiristan ya yi kira ga mutane su rika bin dokar kare kansu

- Stephen Mamza ya na cikin kwamitin da ke yaki da COVID-19 a Jihar

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya na reshen jihar Adamawa, Bishof Stephen Mamza ya na dauke da kwayar cutar COVID-19.

Jaridar The Nation ta ce a halin yanzu Stephen Mamza ya killace kansa, kuma ya fara jinya.

Bishof Mamza shi ne babban Rabaren na cocin mabiya darikar Katolika da ke garin Yola, jihar Adamawa.

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto a ranar 23 ga watan Agusta, 2020, Mamza ya sanar da halin da ya ke ciki ne a ranar Lahadi.

Mamza ya na cikin ‘yan kwamitin da gwamnatin jihar Adamawa ta kafa domin yaki da annobar cutar COVID-19.

KU KARANTA: Za a fara yi wa Mata gwajin shan kwaya kafin su yi aure

COVID-19: Bishof Stephen Mamza ya na dauke da kwayar Coronavirus
Bishof Stephen Mamza Hoto: PM News
Asali: UGC

Limamin cocin ya yi kira ga mutanen jihar da su yarda cewa wannan cuta gaskiya ce, ta na iya harbin mutum.

Shararren malamin katolikan ya bukaci al’umma su rika bin dokokin da masana su ka bada na kauracewa wannan cuta.

“Wani darasi guda da na ke so mutane su dauka shi ne, kowa zai gabatar da kanshi domin ayi masa gwaji, idan hakan ta kama.” Inji Faston.

An rahoto Faston ya na cewa kamuwa da ciwon COVID-19 ba ya nufin mutum ya shiga uku, ya lalace.

A cewarsa Coronavirus ba hukuncin mutuwa ba ce, ya kuma roki jama’a su yi masa addu’ar samun lafiya daga ciwon.

A halin yanzu, Mamza ya ware kansa a dakin jinya, ya na samun kulawar malaman asibiti.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel