Manyan dalilai guda 5 da za su sanya dole Messi ya bar Barcelona

Manyan dalilai guda 5 da za su sanya dole Messi ya bar Barcelona

- Fitaccen dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona na takun saka da shugabannin kungiyar

- An bayyana manyan dalilin da ya sanya dan wasan mai shekaru 33 a duniya yake fushi da kungiyar

- Messi bai ji dadi ba ko kadan da Barcelona ta sayar da Neymar sannan kuma suka kasa sake siyo shi

Har yanzu dai ana ta magana akan halin da ake ciki tsakanin Messi da kungiyarshi ta kwallon kafa ta Barcelona, yayin da ake ta kace-nace bisa rashin masaniya ko dan wasan zai cigaba da bugawa kungiyar wasa a shekara mai zuwa yayin da yake barazanar barin kungiyar.

Dan wasan dan kasar Argentina yana fushi sosai da kungiyar ta shi, inda rahotanni ke nuni da cewa fitaccen dan wasan yana barazanar barin kungiyar baki daya a shekarar 2021.

An gano cewa Messi, wanda kwantiragin shi zai kare a shekarar 2021, ya bayyanawa kungiyar ta kawo sauyi ga 'yan wasan ko kuma ya bar kugniyar.

Haka kuma ya sanar da manajan kungiyar Ronald Koeman cewa yana ganin abincishi ya kare a kungiyar, sai dai kuma ga wasu dalilai da ya sanya fitaccen dan wasan yake fushi da kungiyar, kamar yadda kafar yada labarai ta kasar Spain ta bayyana.

1. Kasa cimma matsaya wajen dawo da Neymar

Duk da samun nasarar zura kwallaye 68 da yayi ga kungiyar ta Barcelona, Neymar wanda yake babban aboki ga Messi an kyaleshi ya koma kungiyar kwallon kafa ta Faransa ta PSG a shekarar 2017.

Tun a wancan lokacin Barcelona tana yin iya bakin kokarinta wajen dawo da dan wasan amma lamarin yaci tura.

2. Korar Valverde

An kori tsohon manajan kungiyar ta Barcelona Ernesto Valcerde a watan Janairu, sakamakon rashin kokari da yayi a kungiyar, inda shi kuma yana da dangantaka ta musamman da Messi.

3. Caccakar da Abidal yayi

Daraktan kungiyar Eric Abidal yayi zargin cewa wasu daga cikin dalilan da suka sanya Valverde ya kasa komai a kungiyar na da nasaba da cewa wasu daga cikin 'yan wasan basa farin ciki da wasa a karkashinsa.

Wannan magana ta batawa Messi rai, inda ya hau shafukan sadarwa ya bayyana cewa: "Dole shugabannin kungiyoyin wasa su gabatar da ayyukansu kamar yadda ya kamata, sannan kuma su dauki alhakin abubuwan da suka yi."

4. Rashin jituwa da Setien

Har ya zuwa lokacin da kocin kungiyar Quique Setien ya fara horar da 'yan wasan, Messi ya kasa samun jituwa da shi kamar yadda suka saba da Valverde.

5. Rage albashi

Messi da sauran 'yan wasan kungiyar sun samu matsala inda aka yanke musu albashi har kusan kashi 70 cikin 100, sakamakon annobar coronavirus, inda shi kuma Messi ranshi ya baci akan yadda aka yi kungiyar har ta bari wannan lamari ya shafi 'yan wasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel