ASUU ta bayyana sharadin janye yajin aiki ga FG

ASUU ta bayyana sharadin janye yajin aiki ga FG

Kungiyar malaman jami'a masu koyarwa (ASUU), ta jaddada cewa za ta ci gaba da yajin aikinta har sai gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta cika alkawurran da ta daukar mata na 2012.

A yayin jawabi ga masu ruwa da tsaki a jami'ar Fatakwal ta jihar Ribas a ranakun karshen mako, shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi, ya ce bukatun kungiyar sahihai ne kuma saboda kasar ta mika su.

Kamar yadda yace, idan aka tabbatar da bukatunsu, dalibai ne za su amfana. Ya yi kira ga daliban da su nuna fahimtarsu a fili.

"Dalibai wadanda 'ya'yanmu ne kuma abokan ci gabanmu yakamata su nuna fahimtarsu, abinda muke bukata daga gwamnati duk don amfanin su ne da kasar baki daya.

"Dakunan kwana masu kyau, dakunan karatu da za su saukaka koyo, dakunan bincike na zamani da kuma ofisoshi da za su tabbatar da ingancin ilimi a jami'a.

"Don haka abinda muke bukata daga gwamnati ba marasa amfani bane. Abubuwan da muka bukata tun a 2012 ne kuma hakan zai tabbatar da ingancin ilimi," jaridar The Nation ta ce inji Ogunyemi.

ASUU ta bayyana sharadin janye yajin aiki ga FG
ASUU ta bayyana sharadin janye yajin aiki ga FG. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Dumu-dumu: Yadda aka kama matasa biyu suna luwadi da junansu

Shugaban ASUU ya jajanta yadda wasu malaman jami'a ke karbar albashi babu kari tun daga 2009 har zuwa 2020.

Ya dauka alwashin matukar ba a shawo kan irin wadannan matsalolin ba, za su ci gaba da yajin aikin.

Ya ce: "Matsalar albashi har yanzu tana nan ba a shawo kanta ba. Mun gano cewa wasu daga cikin jiga-jigai a gwamnati sun sha alwashin wahalar da mu ta hanyar rike mana albashi. Amma muna da tabbacin cewa, matukar muka magance wannan matsalar, sauran za su koma daidai.

"Yarjejeniyar 2008 da muka yi da gwamnati shine duk shekaru uku za mu sake dubata. Amma tun daga nan bamu sake samun damar a duba mana albashi ba. Yakamata a cika alkawurran 2017 sannan a rufe yarjejeniyar.

"A fitar da sabon tsarin albashi kuma muna jaddada cewa sai an kammala shi sannan za mu dakatar da yajin aiki."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel