Sanusi ya yi martani a kan janye gayyatar El-Rufai da NBA ta yi daga taronta

Sanusi ya yi martani a kan janye gayyatar El-Rufai da NBA ta yi daga taronta

Muhammadu Sanusi, tsohon sarkin Kano, ya yi martani a kan janye goron gayyatar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, zuwa taron kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA).

Kungiyar ta janye gayyatarta da ta yiwa El-Rufai matsayin daya daga cikin masu jawabi a taronta bayan rashin amincewar wasu daga cikin lauyoyinta, jaridar The Cable ta ruwaito.

A yayin jawabi ga manema labarai bayan saduwa da El-Rufai a gidan gwamnatin jihar Kaduna a ranar Lahadi, Sanusi ya ce a maimakon janye goron gayyatar gwamnan, da lauyoyin sun yi amfani da wannan damar wurin tattaunawa da gwamnan a kan bangarorin da suke so ya gyara a sha'anin mulkinsa.

"Idan kuna tunanin gwamnan jihar Kaduna baya muku yadda kuke so, kamata yayi ku gayyacesa kuma yayi muku bayani sannan ku sanar da shi cewa baya muku yadda kuke so. Za ku koyi wani abu daga wurinsa, haka shima zai koya wani abu daga wurinku," yace.

"Idan baka jituwa da wani, samunshi tare da sanar da shi abinda ke cikin ranka shine mafita kuma zai iya kare kansa. Idan kuwa akwai abubuwan da ake bukata ya gyara, zai duba. Idan kuwa abubuwa ne da baku fahimta ba, zai yi muku bayani.

"A tunanina NBA ta rasa damar tuhumar gwamnan tare da samun damar tattaunawa da shi don shawo kan matsalolin shugabanci," yace.

Sanusi ya yi martani a kan janye gayyatar El-Rufai da NBA ta yi daga taronta
Sanusi ya yi martani a kan janye gayyatar El-Rufai da NBA ta yi daga taronta. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dumu-dumu: Yadda aka kama matasa biyu suna luwadi da junansu

A yayin tsokaci a kan martanin da ke biyo bayan janye goron gayyatar gwamnan jihar Kaduna, Sanusi ya shawarci NBA da kada ta bar wannan lamarin ya haifar mata da wata matsala ta daban.

"Wannan ce babbar hanyar shawo kan al'amura irin haka. Amma kuma, na ga martanin sassa daban-daban na NBA, ina fatan wannan ba zai haifar da rikici na kabilanci ko addini ba," yace.

Ya kara da cewa, "Nasir yana da ra'ayoyi, ya san ra'ayoyinsa a kan abubuwa masu tarin yawa. Idan ya bayyana matsayarsa, wasu kan so hakan, wasu kan ki ta. Shiyasa ake kiransa da mai wuyar sha'ani.

"Idan kuwa mutum ya zamanto mai wuyar sha'ani, wasu basu son hakan. Wasu na son mutumin da bashi da wuyar tankwasuwa, a hakan sai ka zama baka da abokai ko makiya."

Tsohon basaraken ya jinjinawa El-Rufai, inda yace yana matukar farin ciki da yadda yake jagorantar jihar Kaduna.

Wannan ce ziyarar Sanusi ta farko a arewa tun bayan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya tube masa rawaninsa.

Bayan isowarsa a ranar Lahadi, dubban jama'a sun karba tsohon sarkin inda suka dinga bin tawagarsa suna bayyana goyon bayansu garesa a titunan babban birnin Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel