Yadda na tsere daga hannun ‘yan sanda - Kwararren makashi Shodipe

Yadda na tsere daga hannun ‘yan sanda - Kwararren makashi Shodipe

Kwararren makashi, Sunday Shodipe, ya bayyana yadda ya tsere daga ofishin ‘yan sandan Mokola, Ibadan, jihar Oyo a ranar Talata.

Wanda ake zargin ya ce wata sabuwar shugaba ta reshen, wacce aka kawo ofishin ‘yan sandan kwanan nan ce ta umurci wani jami’i mai suna Funsho da ya bar shi ya yi wanka.

Ya ce jami’in ya gargade shi a kan kada ya yi yunkurin tserewa yayinda yake wanka, inda ya kara da cewa a wannan lokacin shi bai yi tunanin guduwa ba ma.

Shodipe ya bayyana cewa ya yi nasarar tserewa ne lokacin da ya ga cewa hankalin jami’in ya yi nisa wajen tattaunawa da wani mutum kuma baya lura da shi.

Yadda na tsere daga hannun ‘yan sanda - Kwararren makashi Shodipe
Yadda na tsere daga hannun ‘yan sanda - Kwararren makashi Shodipe Hoto: The Cable
Asali: UGC

Ya ce: “wata sabuwar DPO mace da aka kawo ta bukaci Funsho da ya kyale ni na yi wanka. Ya gargade ni a kan kada na yi kokarin guduwa a lokacin da nake wanka.

“Na tsere ne lokacin da naga yana tattaunawa da wani mutum. Na hau saman tuka-tuka sannan ya haura katanga. Mutanen da ke zaune a yankin sun gan ni lokacin da nake tserewa amma basu fallasa ba.”

Sahara Reporters ta tattaro cewa wani matashi daga Akure, jihar Ondo, wanda ya nemi a sakaya sunan shi, ya bayar da kansa domin taimakawa ‘yan sanda lokacin da ya ga labarin cigiyar wanda ake zargin da kuma garabasar da aka sanya kan bankado shi.

Ya ce ya yi tattaki har zuwa Ibadan tare da wasu abokansa uku da niyan farautar mai laifin na kwanaki uku.

Da isar su jihar, sai suka yada zango a wani otel inda suka kwana kafin suka bazama nemansa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kwararren makashi Shodipe ya sake shiga hannu bayan saka kyautar kudi ga wanda ya fallasa shi

An tattaro cewa mutanen uku sun bibiye shi zuwa inda ya siyi tabar wiwi a birnin amma sai suka yanke shawarar kin kama shi saboda dandazon jama’a a yankin.

Daga baya sai ‘yan garin suka kama shi yayinda yake shi kadai a mabuyarsa.

Wanda ake zargin ya kashe kimanin mutum takwas wadanda suka kasance duk mata a karamar hukumar Akinyele da ke jihar Oyo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel