Hotuna da bidiyon Sanusi II a ziyararsa ta farko a arewa bayan saukarsa sarauta

Hotuna da bidiyon Sanusi II a ziyararsa ta farko a arewa bayan saukarsa sarauta

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya sauka a jihar Kaduna bayan sama da watanni biyar da ya kwashe a jihar Legas bayan tube rawaninsa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya yi.

Ziyarar Sanusi jihar Kaduna ce ziyara ta farko da ya kawo wa Arewacin Najeriya tun bayan tube masa rawani a ranar 9 ga watan Maris ta 2020.

Ana tsammanin tsohon abokinsa na sama da shekaru 40, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, zai karbi bakuncinsa a gidan gwamnatin jihar Kaduna.

Hotuna da bidiyon Sanusi II a ziyararsa ta farko a arewa bayan saukarsa sarauta
Hotuna da bidiyon Sanusi II a ziyararsa ta farko a arewa bayan saukarsa sarauta. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

Tsohon Sarkin Kanon ya isa jihar Kaduna inda cincirindon jama'a suka tarbesa tare da nuna murnarsu a bayyane.

Wasu daga ciki sun bayyana fostocin kamfen dinsa na 2023 a jikin motocinsu.

Sanusi tsohon shugaban babban bankin Najeriya ne wanda alakarsu ta yi tsami da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano tun a shekarar 2017.

Magoya bayansa sun yarda cewa, rashin nuna goyon baya ga tazarcen Gwamna Ganduje ce daya daga cikin dalilan da suka sa aka tube masa rawani.

Ana kallon Sanusi a matsayin wanda ya tsaya tsayin daka wurin kawo gyara, kuma ya kasance mai kalubalantar wasu daga cikin dokokin gwamnati, lamarin da yasa ya dinga samun rasin jituwa da 'yan siyasa.

Hotuna da bidiyon Sanusi II a ziyararsa ta farko a arewa bayan saukarsa sarauta
Hotuna da bidiyon Sanusi II a ziyararsa ta farko a arewa bayan saukarsa sarauta. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Katsina: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban APC tare da wasu mutum 3

Hotuna da bidiyon Sanusi II a ziyararsa ta farko a arewa bayan saukarsa sarauta
Hotuna da bidiyon Sanusi II a ziyararsa ta farko a arewa bayan saukarsa sarauta. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Bayan tube masa rawani, El-Rufai ya hadu da tubabben basaraken a Awe, jihar Nasarawa, inda ya samu mafaka bayan fitar da shi da aka yi a jihar Kano.

Gwamna El-Rufai a ranar 13 ga watan Maris, ya isa Awe da ke jihar Nasarawa inda ya hadu da tsohon abokinsa.

Sakamakon yawaitar jami'an tsaro, an bar 'yan jarida su tsaya a nisan mita 200 daga inda aminan junan suke.

Sanusi ya bar Awe inda ya koma jihar Legas bayan wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bada umarnin sakinsa daga jihar Nasarawa.

Mai shari'a Anwuli Chikere ya amince da bukatar da lauyan Sanusi, Lateef Fagbemi, ya mika gabanshi a madadin tubabben basaraken.

Tsohon sarkin Kanon ya garzaya gaban kotun inda ya bukaci kotun da ta bada umarnin sakinsa da gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel