Mamman Daura ya killace kansa a Landan, ya yi magana da Buhari

Mamman Daura ya killace kansa a Landan, ya yi magana da Buhari

Tsohon manajan darakta na jaridar New Nigerian, Mallam Mamman Daura, ya yi magana da dan uwansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari daga inda yake killace kansa a birnin Landan, jaridar The Nation ta ruwaito.

An tattaro cewa an fitar da Daura kasar waje cikin halin rashin lafiya, amma wani bidiyonsa da ya bayyana inda yake hira da shugaban kasar daga birnin Landan, ya nuna cewar yana cikin koshin lafiya inda ya keta sintiri a falon masaukinsa.

Sun yi hirar ne ta wayar tarho a cikin harshen Hausa. Sannan kuma daga bisani ya zauna inda suka ci gaba da tattaunawarsu.

Mamman Daura ya killace a Landan, ya yi magana da Buhari
Mamman Daura ya killace a Landan, ya yi magana da Buhari
Asali: Twitter

Hadimin shugaban kasa na musamman kan dandalin zumunta na zamani, Bashir Ahmad, ya wallafa hoton Daura cikin falo yana hira da Buhari a shafinsa na twitter.

KU KARANTA KUMA: Daga dawowa: ‘Yan Najeriya sun chaa a kan Aisha Buhari saboda ta yi kira ga inganta asibitoci

"Babu kamshin gaskiya a labarin baya na cewa an fitar da Mallam Mamman Daura zuwa Landan domin samun kulawar likitoci cikin gaggawa, yana nan cikin koshin lafiya, ‘yan Najeriya su yi watsi da labarin," Bahir ya wallafa.

A bidiyon an jiyo Daura yana fadin : “Gwamnan din ya zo kwana guda kafin na tafi. ya zo mun gaisa da shi, ya zo ya yi gaisuwar Samaila Isa (Funtua). Eh ranka ya dade, ana gobe tafiyar, eh da gaske ne, amin, amin, lokaci ya yi. Amin, toh.

Kasar Ingila ta wajabtawa sabbin shigowa daga wasu kasashe ciki harda Najeriya killace kansu na kwanaki 14.

A baya mun ji cewa wani hadimi kuma makusancin Mamman Daura, Aminu Balele Kurfi, ya bayyana makasudin tafiyarsa Landan.

A cewar Balele Mamman Daura wanda ya kasance dan uwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tafi birnin Landan ne domin duba lafiyarsa kamar yadda ya saba lokaci zuwa lokaci.

Mista Kurfi na martani ne ga rahotannin ranar Laraba da ke cewa an garzaya da Mamman Daura Landan sakamakon wata rashin lafiya da ake zargin korona ce.

Da yake zantawa da jaridar Premium Times a yammacin Laraba, Kurfi ya ce: “duniya gaba daya ta ga Mamman Daura lafiyarsa kalau a ranar Talata, lokacin da ya halarci sallar jana’izar marigayi Wada Maida.”

Ya kuma ce Daura kan fita duba lafiyarsa lokaci zuwa lokaci a wajen tsoffin likitocinsa da ke zama a Ingila.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel