Daga dawowa: ‘Yan Najeriya sun chaa a kan Aisha Buhari saboda ta yi kira ga inganta asibitoci

Daga dawowa: ‘Yan Najeriya sun chaa a kan Aisha Buhari saboda ta yi kira ga inganta asibitoci

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta dawo gida Najeriya daga kasar Dubai a ranar Asabar, sannan ta yi kira ga inganta asibitocin kasar.

Amma ‘yan Najeriya da dama sun fusata da wannan bukata nata, inda suka zarge ta da rashin tunani.

Wasu daga cikinsu sun bayyana wannan bukata nata a matsayin “abun kunya da cin mutunci.”

Jaridar Punch ta ruwaito cewa uwargidar shugaban kasar ta je kasar Dubai a farkon makon watan Agusta sakamakon ciwon wuya da ta yi fama da shi.

Da dawowarta, ta nemi ma’aikatan cibiyyoyin lafiya da su yi amfani da damar shirin gwamnatin tarayya na bayar da bashin naira biliyan 100 ga fannin lafiya.

Daga dawowa: ‘Yan Najeriya sun chaa a kan Aisha Buhari saboda ta yi kira ga inganta asibitoci
Daga dawowa: ‘Yan Najeriya sun chaa a kan Aisha Buhari saboda ta yi kira ga inganta asibitoci Hoto: Aisha Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Taron NBA: A janye gayyatar da aka yi wa Obasanjo da Wike suma – Kungiyar lauyoyi Musulmai

Cewa “shakka babu hakan zai taimaka wajen ginawa tare da habbaka fannin lafiya na Najeriya sannan hakan zai rage yawan fita kasashen waje don ganin likita.”

Da yake martani ga furucin Aisha Buhari, wani mai amfani da shafin Twitter Bulama Burkati ya ce: “mijinki ya kashe makudan kudade a kan asibitin Villa, amma aka gaza magance ‘ciwon wuya’ a asibitin

“Kin lula kasar Dubai a lokacin kulle. Da dawowarki, kina kira ga asibitoci masu inganci. Baki san wanene shugaban kasar ba? Ba ki da ikon ganinsa ne?”

Mosh @mosh_aloaye ya kara da cewa : “Wannan abun bakin ciki ne. Yanzu ta bar Najeriya a lokacin da ake tsaka da hana fita waje saboda ganin likita sannan ta dawo tana fadin cewa a gyara fannin lafiyar Najeriya. Ina ganin hakan a matsayin cin mutunci matuka.”

Goddy @i2much4dem ya nuna mamaki kan dalilin da yasa ba za a inganta asibitin fadar shugaban kasa ba ta yadda zasu iya magance ciwon wuya.

“Kuma wannan matar shugaban kasa ce. Wani irin gyara asibitin Aso Rock ke bukata domin ya fara aiki? Amma duk da haka Aisha ta lula kasar waje domin jinya”

“Kawai Aisha Buhari na yi wa ‘yan Najeriya ba a ne ta hanyar kira ga inganta asibitoi a kasar alhalin ta san cewa mijinta ne shugaban kasa kuma shine wanda zai bamu ingatattun asibitoci. Kawai dai shugaban kasar da ahlinsa basa yiwa ‘yan Najeriya adalci,” in ji TheRoy @BarrROUN1990

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel