Katsina: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban APC tare da wasu mutum 3

Katsina: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban APC tare da wasu mutum 3

- Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun shiga gundumar Dantankari da ke karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina

- Kamar yadda rahotanni suka bayyana, masu garkuwa da mutanen sun shiga kauyen a daren Alhamis

- Sun iza keyar shugaban jam'iyyar APC, Alhaji Shafi'u Dantankari, wata matar aure da 'ya'yan mijinta biyu

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na gundumar Dantankari da ke karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina.

Jaridar Katsina Post ta gano cewa, 'yan bindigar sun shiga garin ne da daren Alhamis kuma sun yi garkuwa da shugaban jam'iyyar mai suna Alhaji Shafi'u Dantankari.

Hakazalika, 'yan bindigar sun hada da wata matar aure tare da 'ya'yan kishiyarta biyu suka yi awon gaba da su.

Har a lokacin da aka wallafa wannan rahoton, ba a ji koda labarin inda wadanda aka sacen suke ba.

Katsina: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da shugaban APC tare dawasu mutum 3
Katsina: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da shugaban APC tare dawasu mutum 3. Hoto daga Katsina Post
Asali: Twitter

KU KARANTA: Borno ta karba mutum 94 da suka yi nasarar tserowa daga hannun Boko Haram

A wani labari na daban, wasu bakin haure guda uku da suke shigowa da 'yan ta'addar dake yankin Arewa maso Yamma makamai sun shiga hannu, bayan jami'an hukumar soji dake kula da hiyyar jihar Sokoto sun cafke su.

Mai magana da yawun helkwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar John Enenche, yace masu laifin wadanda suka yi shiga irinta 'yan Najeriya an kama su da makamai a kauyen Dantudu dake Mailailai cikin karamar hukumar Sabon Birni dake jihar Sokoto.

Makaman da aka samu a wajensu sun hada da bindiga mai kirar AK-47 guda shida, harsashi guda 2,415, inda duka aka samo su a cikin abubuwan hawan da suke amfani da su wajen tafiye-tafiyensu.

An kuma gano cewa wadanda ake zargin suna hannun jami'an tsaron ana cigaba da gabatar da bincike akansu, inda daga baya za a mika su ga hukumar da ta dace domin yi musu hukunci.

Enenche ya kara da cewa: "Hakan na nuni da cewa wasu matsalolin tsaron dake faruwa a Najeriya akwai sa hannun mutanen da ba 'yan kasar ba. Wadanda ake zargin yanzu suna hannu ana cigaba da gabatar da bincike akan su kafin a danka su a hannun hukumar da ta dace domin gabatar da hukunci a kansu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel